Dattijo mai shekaru 70 ya shiga da laifin Luwadi a jihar Jigawa

Dattijo mai shekaru 70 ya shiga da laifin Luwadi a jihar Jigawa

Wani Dattijo mai shekaru 70 a duniya can jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, ya shiga hannun jami'an hukumar tsaro ta NSCDC dumu-dumu da aikata babban laifi na Luwadi da ya kasance daya daga munanan laifuka na yiwa kasa fasadi.

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, wannan Baragurbin Dattijo, Umaru Abubakar, ya shiga hannu dumu-dumu yayin da yake tsaka da zakkewa wani Matashi mai shekaru 20 a duniya ba bu ko tsoron Mahaliccin su Madaukakin Sarki.

Cikin sanarwar kakakin rundunar hukumar NSCDC na jihar, SC Adamu Shehu, ya bayyana cewa Umaru wanda mazauni ne a Unguwar Makwalla da ke karamar hukumar Birnin Kudu, ya shiga hannun tare da abokin tarayyar sa na unguwar Zarenawa su na tsaka da aikata mummunar alfasha.

Jami'an hukumar NSCDC na atisaye
Jami'an hukumar NSCDC na atisaye
Asali: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, 'yan kungiyar Bijilanti ke da alhakin damke wannan miyagu biyu da misalin karfe 11.00 na Yammaci a cikin Babbar Kasuwar garin Birnin Kudu su na tsaka da Tumasanci.

Kazalika kakakin rundunar hukumar ta NSCDC ya kara da cewa, wani Matashi Ismaddeen Datti mai shekaru 21, ya shiga hannu tare da wani Saurayi dan shekaru 14 da laifin mummunar ta'ada ta neman Maza.

KARANTA KUMA: Zaben Gwamnoni: Buhari zai ziyarci jihar Akwa Ibom da Imo

Cikin wani rahoton da shafin jaridar Legit ta ruwaito ya bayyana cewa, wutar gobara da sanyin safiyar jiya ta Lahadi, ta kone wani Magidanci, Mai dakin sa da 'ya'yan su uku a unguwar Hausawa da ke birnin Kanon Dabo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel