Kwanan nan NNPC za ta fara hakar man fetur a arewa - Buhari

Kwanan nan NNPC za ta fara hakar man fetur a arewa - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar nan da kankanin lokaci Hukumar Tace man fetur na kasa NNPC zata zurfafa neman man fetur da iskar gas a wasu yankunan na jihar Benue da ke Arewacin Najeriya.

Shugaban kasar ya ce wannan shine mataki na biyu a yunkurin fara hako man fetur din bayan gano akwai mai a kusa da rafin Kolmani da ke jihohin Bauchi da Gombe.

A sakon da hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya ce Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin da ya ke ganawa da Shugabanin gargajiya da dakin taro na Banquet da ke gidan gwamnati a Makurdi na jihar Benue.

Kwanan nan NNPC za ta fara hakar man fetur a arewa - Buhari
Kwanan nan NNPC za ta fara hakar man fetur a arewa - Buhari
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

Shugaban kasar ya ce tun lokacin da ya ke Ministan man fetur a 1970s, ya ga binciken neman man fetur maso ban sha'awa da ke nuna akwai yiwuwar samun man fetur da iskar gas daga Tafkin Chadi zuwa Benue da Delta.

Ya ce amma saboda kasuwanci da cinnikayya, an mayar da hankali a yankin Neja Delta domin samun sakamako a cikin gaggawa.

Ya bayar da bayyanin kokarin da ya yi a matsayinsa na Shugaban kasa na mulkin soja domin domin ganin an mayar da hankali ga dukkan jihohin da ake tsamanin samun man fetur inda ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta cigaba da hakan.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma yi yi godiya bisa ga jawabin da Tor Tiv, Mai Martaba Farfesa James Ayatse ya yi inda ya ce an samu saukin rikicin makiyaya da manoma a jihar kuma ya yabawa yadda shugaban kasar ke gudanar da kamfen dinsa cikin zaman lafiya.

Shugaban kasan kuma ya yi alkawarin duba bukatar gina karin tituna, gadoji da makarantun gaba da sakandare da basaraken ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel