An Dauki Bidiyon Jagoran Jam'iyyar Su Kwankwaso Ya Tuɓe Kaya Ya Shiga Kogi

An Dauki Bidiyon Jagoran Jam'iyyar Su Kwankwaso Ya Tuɓe Kaya Ya Shiga Kogi

  • Jagoran jam'iyyar NDC ba kasa, Sanata Seriake Dickson ya ja hankali lokacin da ya shiga ruwa ya yi iyo a Kogin Forcados da ke yankinsa na Bayelsa
  • Tsohon gwamnan Bayelsa ya ce ya taso a kusa da kogin har ya kai shekara 20, kuma suna yawan zuwa iyo a ruwan
  • Ya bukaci matasa su koyi iyo domin yana da amfani a matsayin wasanni da kuma kwarewar ceton rai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa, Nigeria - Sanata Seriake Dickson, mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya kuma jagoran jam'iyyar NDC ya shiga Kogin Forcados ya yi iyo domin tuna baya

Dickson, tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, ya bayyana cewa ya ji dadin komawa kogin da ya taso a kusa da shi, inda ya shafe wani bangare na rayuwarsa tun yana yaro har ya kai shekara 20.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi ya kashe mahaifinsa shugaban APC a yanayi mai tada hankali

Dickson.
Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Duckson lokacin ds ya yi tsalle ya afka cikin kogi a jihar Bayelsa Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Jagoran NDC ya shiga ruwa a Bayelsa

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X hade da bidiyon shigarsa kogin ranar Litinin, tsohon gwamnan ya ce ziyarar ta ba shi damar komawa wani muhimmin wuri da ke da alaka da tarihinsa da kuma lokacin yarintarsa.

Ya ce ya tube kaya ya shiga kogin ne domin yin iyo, kuma ya ji dadin wannan lokaci da ya samu a cikin al’ummarsa.

“Yau na ziyarci kogin da na taso a kusa da shi har zuwa lokacin da na kai shekara 20. Na shiga cikinsa na yi iyo a Kogin Forcados, a nan cikin al’ummata, kuma na ji dadin hakan sosai,” in ji Dickson.

Dickson ya fadi muhimmancin iyo

Sanatan ya kuma bayyana cewa yin iyo na daga cikin abubuwan da yake morewa lokaci zuwa lokaci tare da yaransa.

Ya ce dukkan yaransa sun koyi yadda ake iyo, lamarin da ke nuna cewa yana daukar wannan kwarewa a matsayin wani abu mai muhimmanci da ya kamata yara su koya.

Kara karanta wannan

Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe

A cewarsa, shiga ruwa ba wai hanya ce ta motsa jiki ko nishadi kadai ba, yana kuma da amfani wajen taimaka wa mutum ya kare kansa idan ya shiga cikin ruwa.

Dickson ya bukaci matasa maza da su ba da muhimmanci wajen koyon iyo, musamman wadanda ke zaune a yankunan da koguna da sauran wuraren ruwa suke da yawa.

Dickson.
Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar dattawa, Seriake Dickson Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook
“Ina karfafa gwiwar dukkan samari su koyi yin iyo. Ba wai wasa ne mai kyau kawai ba, har ila yau muhimmiyar kwarewa ce ta rayuwa, musamman ga mu da muke zaune a yankunan da ke kewaye da ruwa,” in ji shi.

Kalaman sanatan sun jaddada muhimmancin koyon dabarun da mutum zai iya amfani da su wajen kare kansa a rayuwar yau da kullum.

Sanata Dickson ya hango faduwar Tinubu

Kun ji cewa jagoran NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya ce shugaba Bola Tinubu da APC za su sha kaye idan aka gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya.

Sanatan ya buƙaci a bai wa dukkan jam'iyyun adawa damar shiga zaɓe ba tare da jawo masu matsala ba, yana mai cewa sun shirya tsaf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262