Pantami, Fasto Bakare da Mutane 5 da Suka Ki Karbar Mukamin Gwamnatin Tinubu

Pantami, Fasto Bakare da Mutane 5 da Suka Ki Karbar Mukamin Gwamnatin Tinubu

  • Wasu manyan ’yan Najeriya sun ki karbar mukamai daga Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayan hawansa karagar mulki
  • Wasu sun bayyana cewa sun gaji da ayyukan gwamnati, wasu kuma sun fi son a ba wasu damar rike matsayi a birnin Abuja
  • Akwai Moses Ayom wanda ba a kai ga yi masa tayin ba sai ya toshe kofar domin gudun jiharsa ta rasa babban matsayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Akwai wasu da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi wa tayin mukami a Gwamnatin Tarayya amma suka ki karba ko suka nuna ba za su so ba.

Ba wannan ne karon farko da aka yi haka ba, ko a lokacin marigayi Muhammadu Buhari akwai wadanda suka ki karbar tayin mukami a gwamnatinsa.

Mutanen da ba su son mukamin Bola Tinubu

Lura da labarin da ya fito daga bakin Tunde Bakare, Legit Hausa ta shiga binciken duk shugabanni da ‘yan siyasa da suka ki yarda su yi aiki da Tinubu.

Kara karanta wannan

Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe

1. Ayodele Fayose

A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels, Ayodele Peter Fayose ya bayyana cewa an nemi ya yi aiki da gwamnatin Bola Tinubu amma bai amsa ba.

Tsohon gwamnan Ekiti ya ce shugaban kasa ya tambaye shi me yake so, amma ya fada masa a shekaru 65, bai neman komai illa ya koma gida abinsa.

2. Orji Uzor Kalu

Tun a farkon gwamnati mai-ci, Orji Uzor Kalu ya ce an yi masa tayin zama minista da bai samu kujerar shugaban Majalisar dattawa ba, amma ya ki karba.

Sanatan ya shaida cewa ya bukaci shugaba Tinubu ya zabi duk wanda yake so daga Abia. Daga karshe sai Nkiru Onyejiocha ta wakilci jihar a majalisar FEC.

3. Isa Ali Pantami

Shi Isa Ali Pantami ya ce har sau uku shugaban Najeriya yana yi masa tayin matsayi a Gwamnatin tarayya, shi ma ya zabi ya cigaba da yin harkokin gaban sa.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru, Amaechi ya fito da yadda suka yi da Buhari kan wanda yake so ya gaje shi a 2023

Tsohon ministan ya yi wadannan bayani ne da aka nemi a yi masa gori a APC lokacin da ya je sabunta katin jam’iyyarsa a Gombe a cewar Premium Times.

4. Urum Kalu-Eke

A shekarar 2024 da aka zabi Urum Kalu-Eke ya shiga cikin Majalisar da ke kula da aikin bankin CBN, ya ki karbar mukamin yana cewa za su ci masa karo da aikinsa.

The Nation ta rahoto shi ya ce a matsayinsa na wanda yake aiki da Bankin Duniya da wasu kamfanoni masu zaman kansu, ba zai iya karbar mukamin ba.

5. Fatima Alkali

An so Farfesa Fatima Alkali ta zama Kwamishina a hukumar NLRC mai gyara harkokin shari’a, amma ta nuna ba ta sha’awar wannan kujera ta gwamnati.

A wani rahoto na The Cable aka ji Sanata Adeniyi Adegbonmire ya ce farfesar ta sanar da Fadar shugaban kasa ba za ta karbi aikin ba, ba a san dalilin ta ba.

6. Moses Ayom

Akwai irinsu Cif Moses Ayom da suka yi ikirarin an yi kira da a nada shi minista amma ya yi watsi da wannan magana ba don ya fi karfin rike mukamin ba.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna Abba ya samu tauhidi a batun koma wa mulkin jihar Kano

Ko da bai ce an kai ga yi masa tayi ba, tsohon jagoran na APC ya ki karbar shawarar saboda Sanata George Akume ya zama Sakataren gwamnati in ji Independent.

7. Tunde Bakure

Mun rahoto Tunde Bakare kwanan nan yana cewa an so ya zama minista a gwamnatin Tinubu sai dai ya ki yin na’am da hakan saboda ganin tsufa ya kama shi.

Abokin takarar na marigayi Muhammadu Buhari a 2011 ya yi alkawarin zai cigaba da taimakon jam’iyyar APC da shawarwari kuma ba zai sauya sheka ba.

Wahalar da Isa Pantami ya sha a takara

An kawo rahoton wahalar da Isa Ali Ibrahim Pantami ya sha tun daga APC zuwa PDP da kuma a hannun INEC kafin a ce shi ne ‘dan takarar gwamna a Gombe.

Kafin a je ko ina wasu 'ya 'yan APC a jihar Gombe suna cewa malamin ba 'dan siyasa ba ne, wasu kuma suka ce bai tuna da su ba tun da ya samu mukami a Abuja.

Da ya gagara samun yadda yake so a APC kuwa, an ji matsalolin da ya samu ko da ya shiga jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng