Magana Ta Kare: Trump Ya Yi Maganar Yiwuwar Sake Kai Hare Hare a Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce da wuya a sake barkewar faɗa tsakanin Amurka da Iran, amma ya danganta hakan da amincewar Tehran da wata yarjejeniya mai ƙarfi
- Trump zai gana da Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, a Fadar White House domin tattauna batun da ya shafi rikicin
- Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce an dakatar da zirga-zirgar masu shiga tsakani yayin da ake nazarin sakamakon zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya nuna shakku kan yiwuwar sake barkewar faɗa tsakanin ƙasarsa da Iran.
Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa sake kai hare-hare a Iran ba abu ne mai yiwuwa sosai ba.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar CNN ranar Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026 gabanin ganawarsa da Firaministan Qatar, wanda ke shiga tsakani a rikicin, ranar Litinin.
Sai dai shugaban Amurkan ya yi gargaɗin cewa matakin da zai ɗauka zai dogara ne kan ko Iran za ta amince da wata yarjejeniya mai ƙarfi.
Trump ya danganta zaman lafiya da yarjejeniya
A cikin makonnin baya-bayan nan, Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta iya sake kai hare-hare kan Iran.
Wasu rahotannin kafafen yaɗa labaran Amurka ma sun nuna yiwuwar sake barkewar faɗa bayan zaɓen tsakiyar wa'adin majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar ranar Talatar da ta gabata. Sai dai Trump ya bayyana wa tashar cewa sake faɗan abu ne da ba ya ganin zai faru cikin sauƙi.
"Zan iya yin hakan idan ya zama dole, amma mun kai musu hari sosai. Na farmake su ƙwarai da gaske. Ba ku san irin ƙarfin harin da na kai musu ba.” In ji shi.
Trump zai gana da Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, a Fadar White House ranar Litinin.
Al Thani, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen Qatar, na cikin waɗanda ke shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran domin neman mafita ga rikicin.
Wannan ce ganawar Trump ta farko da wani shugaban ƙasar waje tun bayan babban koma-bayan da jam'iyyar Republican ta sha a zaɓen tsakiyar wa'adin, inda ta rasa ikon tafiyar da Majalisar Dokokin Amurka.
Iran ta ce an dakatar da tattaunawar zaman lafiya
A nasa ɓangaren, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa an dakatar da tattaunawar zaman lafiya na ɗan lokaci yayin da ake nazarin tasirin sakamakon zaɓen Amurka.
Ya ƙara da cewa dole ne a jira a ga tsawon lokacin da Amurkawa za su ɗauka kafin su fahimci sakamakon zaɓen, domin a san yadda za a ci gaba da tattaunawar.
Iran ta danganta shan kaye na Republican da yaƙin
Trump ya amince cewa yaƙin da ake yi da Iran, wanda bai samu karɓuwa sosai a tsakanin jama'ar Amurka ba, ya taimaka wajen jawo wa jam'iyyar Republican rashin nasara a zaɓen.
Rikicin ya fara ne a ƙarshen watan Fabrairu, bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran.
A ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026, Araghchi ya ce Trump ya fahimci cewa yawancin Amurkawa ba sa jin daɗin Isra'ila.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ministan ya ce:
“A bayyane yake cewa Amurkawa sun gaji da yadda Isra'ila ke yaudarar gwamnatocin Amurka domin jefa su cikin yaƙe-yaƙe marasa ƙarewa. Sun ƙoshi da hakan. Haka ma yankinmu ya ƙoshi.”

Source: Getty Images
Trump ya yi maganar shiga aljanna
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen korar baƙi daga ƙasar sun yi tsauri.
Da aka tambaye shi ko yana ganin zai shiga Aljanna, shugaban ya ce shi mutum ne mai addini, don haka yana fatan hakan zai kasance.
Asali: Legit.ng


