Jam'iyyar ADC Ta Ragargaji APC kan Hukuncin Rusa Takarar Atiku a Kotu

Jam'iyyar ADC Ta Ragargaji APC kan Hukuncin Rusa Takarar Atiku a Kotu

  • Jam’iyyar ADC ta ƙalubalanci jam’iyyar APC mai mulki da ta gwada farin jininta a zaɓe maimakon amfani da kotuna wajen hana ’yan adawa shiga zaɓen 2027
  • Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Sanata Austin Akobundu, ya ce tarbar da aka yi wa Atiku Abubakar a Sokoto ta rikita APC
  • ADC ta zargi gwamnatin tarayya da APC da ƙoƙarin hana ta shiga takara ta hanyar shigar da ƙara a kotu, inda ta buƙaci a bar ’yan Najeriya su yi zaɓe cikin ’yanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta kalubalanci jam’iyyar APC mai mulki da ta gwada ƙarfin farin jininta a rumfunan zaɓe, maimakon amfani da shari’o’in kotu wajen hana ta shiga zaɓen 2027.

Daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Sanata Austin Akobundu, ne ya yi wannan jawabi a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku, Shettima ya ce tamkar Obi ba ya cikin takarar 2027 ne a yanzu

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku Abubakar a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto ya ce tarbar da aka yi wa ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar, Atiku Abubakar, a jihar Sokoto, da mataimakinsa, Rotimi Amaechi, a jihar Kebbi, na nuna yadda jama’a ke ƙara nuna sha’awar jam’iyyar.

Akobundu ya gode wa magoya baya da mazauna jihohin biyu bisa fitowa da suka yi domin tarbar ’yan takarar, tare da zargin gwamnatin tarayya da APC da ƙoƙarin hana ADC shiga fafatawar siyasa ta hanyar shari’ar kotu.

Jagora a ADC ya kalubalanci APC kan 2027

Akobundu ya ce idan APC ta amince tana da ƙarfin lashe zaɓe, to ya kamata ta bari a gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, ba tare da tsoratarwa ko hana wasu shiga fafatawar ba.

Ya zargi jam’iyya mai mulki da ƙoƙarin amfani da wata hanya ta bayan fage a kotu domin cire ADC daga cikin jam’iyyun da za su fafata a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya yi wa yankin Tinubu gori kan kuri'u, ya bugi kirki kan Arewa

Ya ce ya kamata a bar ’yan Najeriya su saurari manufofin jam’iyyu daban-daban, halartar gangamin siyasa da kuma zaɓar shugabanninsu ba tare da katsalandan ba.

ADC ta bukaci kare dimokuraɗiyya

Daraktan yaƙin neman zaɓen ya jaddada cewa zaɓe ya kamata ya kasance hanyar da jama’a ke amfani da ita wajen bayyana ra’ayinsu da zaɓar shugabannin da suke so.

Ya ce dole ne a bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar gudanar da kamfen cikin ’yanci, domin ’yan Najeriya su yanke shawara bisa abin da suka ji daga gare su.

Akobundu ya kuma buƙaci magoya bayan ADC da kada su bari rikicin siyasar da ake ciki ya ɗauke hankalinsu daga ayyukan neman goyon bayan jama’a.

Nafiu Bala na tsagin ADC
Nafiu Bala d aya shigar da ADC kara kotu. Hoto: Hon. Nafiu Bala
Source: Facebook

Ya bukace su da su ci gaba da kamfen cikin lumana da kwarin gwiwa, yana mai cewa burin al’umma ne ya kamata ya yi nasara.

Kiran jam'iyyar APC ga ADC

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC ta buƙaci ɓangaren ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark ya magance rikicin cikin gida maimakon ci gaba da zargin jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fito ya yi maganganu kan rusa takarar Atiku

APC ta bayyana cewa ba ta da hannu a shari’ar da ta kai ga hukuncin Babbar Kotun Tarayya game da rushe shugabancin ɓangaren Mark.

Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce rikicin na cikin gida ne na ADC, kuma jam’iyya mai mulki ba ta da alaƙa da shari’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng