Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya bayyana wa AMNESTY mawuyacin halin da ya ke ciki

Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya bayyana wa AMNESTY mawuyacin halin da ya ke ciki

A yammacin ranar Laraba ne kungiyar kare hakkin bil’adama ta ‘Amnesty International' ta fara tattara sa hannun jama’a a fadin duniya domin neman a tursasa gwamnatin jihar Kano janye karar da ta shigar da dan jaridar nan, Jafar Jafar, da ya saki faifan bidiyon da ke nuna gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na karbar wasu kudade da ake zargin cin hanci ne daga hannun ‘yan kwangila.

Kungiyar ta Amnesty ta shiga batun ne bayan Jafar ya aike ma ta da wasikar bayanan irin tsangwamar da ya ke fuskanta da kuma irin zaman dar-dar da ya ke yi tun bayan da ya watsa faifan bidiyon a yanar gizo ta shafin kamfanin jaridar sa.

A cikin wasikar, dan jaridar ya bayyana cewar, “Suna na Jaafar Jaafar, dan jarida kuma editan jaridar yanar gizo mai suna ‘Daily Nigerian’ da ke da matsuguni a Abuja.

A watan Oktoba na shekarar 2018, na wallafa wasu faifan bidiyo guda biyu da ke nuna daya daga cikin gwamnonin jihohin arewa na karbar cin hanci daga wurin ‘yan kwangila.

Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya bayyana wa AMNESTY mawuyacin halin da ya ke ciki
Jafar Jafar yayin da ya dira a majalisar dokokin jihar Kano
Asali: Depositphotos

“Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyace ni domin na rantse a gaban ta a kan sahihancin faifan bidiyon bayan sun fara bincike a kan lamarin.

“Sun yi kokarin bani cin hancin makudan kudi domin na janye faifan bidiyon daga shafin jarida ta, har alkawarin ba ni dalar Amurka miliyan biyar an yi.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari: Kwamitin sulhun Abdulsalam ya gana da Atiku da Obi

“A ranar da zan bayyana a gaban majalisar, an debo hayar ‘yan daba domin su ci mutuncin ma su ba ni larfin guiwa. Sannan sun debo daliban makarantar firamare domin su gudanar da zanga-zanga.

“Tun bayan wannan lokaci ni da iyalina ke cigaba da samun barazana kala-kala daga gwamnatin jihar Kano. Na cigaba da aikina na jarida, amma har yanzu ina fuskantar tuhuma a kotu. Ina son ku fada wa gwamnatin jihar jihar Kano ta janye dukkan wata tuhuma da ta ke yi min a gaban kotu. Dole su daina tsangwama da gurfanar da ‘yan jarida.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel