Kamfen: Jama'a sun wulakanta gwamna Badaru na jihar Jigawa

Kamfen: Jama'a sun wulakanta gwamna Badaru na jihar Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa, Mohammad Badaru Abubakar, ya kunyata a yau, Talata, bayan jama'a da dama sun kaurace wa wurin taron yakin neman zaben sa a karamar hukumar Gagarawa.

A yau, Talata, ne aka shirya yakin neman sake zaben Badaru a matsayin gwamna jihar Jigawa a karo na biyu a kananan hukumomin Gagarawa da Kazaure.

A ranar 21 ga watan Janairu ne gwamna Badaru ya kaddamar da yakin neman zaben sa a kananan hukumomin Guri da Hadejia.

Akwai 'yan takara 17 da ke takarar kujerar gwamna a jihar Jgawa. Sai dai 'yan takarar jam'iyyar SDP, Bashir Adamu, da na jam'iyyar PDP, Malam Aminu Ringim, sun fi zama barazana ga takarar gwamna Badaru a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Majiyar Legit.ng ta shaida ma ta cewar jama'ar karamar hukumar Gagarawa sun kaurace wa wurin taron yakin neman zaben gwamnan ne domin nuna fushin su a kan kwace ma su gonaki da gwamnati ta yi tare da bawa wasu bakin haure damar yin noman rani.

Kamfen: Jama'a sun wulakanta gwamna Badaru na jihar Jigawa

Kamfen din Buhari a Jigawa
Source: Twitter

Idris Garin-Ciroma, wani mazaunin karamar hukumar ya ce jama'ar da aka karbi gonakin su na zargin gwamnatin jihar da nuna ma su fin karfi, saboda ba a biya su kudin fansar gonakin su ba.

"Rashin adalcin da gwamnatin mai girma gwamna ta yi mana ne ya sa mu ka zabi kaurace wa wurin kamfen din sa," a cewar Idris.

Da ya ke gabatar da jawabi ga tsirarun jama'ar da su ka halarci wurin taron kamfen din, gwamna Badaru ya kare kan sa a kan abinda ya faru.

DUBA WANNAN: Fallasa: Shigar Atiku Amurka alfarma ce ta wucin gadi - Rahoton Reuters

"Na san kuna fushi da ni a kan abinda ya faru, amma ni fata na shine mu yi nisan kwana, don na tabbata watarana za ku yabe ni a kan abinda ya faru," a kalaman gwamna Badaru.

Kazalika, gwamnan ya bayar da misali da faruwar kwatankwacin irin wannan lamari a jihar Kano, karkashin mulkin Audu Bako, a tsakanin shekarar 1964 zuwa 1975.

Audu Bako, tsohon gwamnan jihar Kano a karkashin mulkin soji, ya karbi gonakin jama'a da dama a karamar hukumar Kura domin amfani da su wajen noman rani.

Duka da karamar hukumar Kura ta yi fice wajen noman rani, musamman noman shinkafa, rahotanni sun ce ya fuskanci tirjiya da kunkuni daga hannun jama'ar da aka karbi gonakin su a wancan lokacin.

A yayin da gwamna Badaru ke gudanar da taron yakin neman zaben, dumbin jama'a sun yi dafifi a Garin-Ciroma, hanyar da gwamnan zai bi wajen fita daga karamar hukumar Gagarawa, tare da gudanar da zanga-zangar nuna fushin su bisa karbe ma su gonaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel