Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Nemi Shugaban INEC Ya Gabatar da Takardun Takarar Tinubu

Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Nemi Shugaban INEC Ya Gabatar da Takardun Takarar Tinubu

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci shugaban INEC, Joash Amupitan, ya gabatar da takardun takarar Shugaba Bola Tinubu na 1999 da 2023
  • Kotun ta kuma umarci Amupitan ya gurfana a matsayin shaida a shari’ar Omoyele Sowore, wanda DSS ke tuhuma kan wasu saƙonnin da ya wallafa
  • Alƙali Mohammed Umar ya dage sauraron shari’ar zuwa 11 ga Nuwamba domin halartar shaidun da masu kare Sowore suka nema

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Joash Amupitan, ya gurfana a gabanta a matsayin shaida.

Kotun ta umarci Amupitan ya gabatar da takardun takarar Shugaba Bola Tinubu na zaɓen gwamnan Jihar Legas na 1999 da na zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a shari’ar da ake yi wa Omoyele Sowore.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito bayan shekaru 5, kotu ta sallami wanda ake zargi da kashe matarsa a Kano

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zaune a wurin tari a fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa takardar sammaci mai taken “Subpoena Duces Tecum” da kotun ta bayar ta shafi lambar shari’a FHC/CR/484/2025.

An aika ta ne ga shugaban INEC, kuma alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mohammed Umar, ne ya sanya hannu a kanta.

Kotun ta umarci Amupitan da ya bayyana domin bada shaida a shari’ar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ke yi wa Sowore kan wasu saƙonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ake zarginsa ya kira Tinubu da “babban ami laifi”.

Takardun da kotu ta nema

A cikin sammaci, kotun ta bukaci Amupitan ya gabatar da takardar INEC Form CF001 da Tinubu ya miƙa wa hukumar a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan Jihar Legas a shekarar 1999.

Takardar da ake nema ta ƙunshi takardar rantsuwa da ta shafi batun takardun shaidar karatu da aka ce sun ɓace.

Haka kuma, kotun ta bukaci shugaban INEC ya gabatar da Form CF001 ɗin da Tinubu ya miƙa wa hukumar a lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da ya soke takarar Atiku a zaɓen 2027

Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotun ta yanke a ranar Litinin, inda ta amince da buƙatar masu kare Sowore na gayyatar Amupitan da Joe Igbokwe, tsohon sakataren yaɗa labarai na APC a Legas, domin su bayar da shaida.

A zaman kotun na ranar Litinin, Ruben Adakole, lauyan Sowore, ya sanar da alƙali cewa ɓangaren masu kare wanda ake tuhuma na da niyyar kiran mutanen biyu domin su bayar da shaida a shari’ar.

Bayan sauraron buƙatar, alƙalin ya amince da ita tare da bayar da umarnin a fitar da sammacin gayyatar mutanen biyu.

Kotun ta soke sammacin lauyan DSS

A wani hukunci daban, kotun ta yi watsi da buƙatar Sowore ta tilasta wa Akinlolu Kehinde, babban lauyan DSS, ya bayyana a matsayin shaidar masu kare wanda ake tuhuma.

Amupitan.
Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Nemi Shugaban INEC Ya Gabatar da Takardun Takarar Tinubu
Source: Facebook

Alƙalin ya kuma soke sammacin da aka bayar a baya domin tilasta wa Kehinde bayyana a kotun, yana mai cewa lauyoyi na da nauyin kare sirrin tattaunawarsu da waɗanda suke wakilta.

A ƙarshe, alƙalin ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga Nuwamba domin Amupitan da Igbokwe su bayyana a matsayin shaidun masu kare Sowore.

SERAP ta maka INEC a kotu

Kara karanta wannan

"APC da Shugaba Tinubu sun fara fargabar haɗuwa da Atiku a babban zaben 2027"

Kun ji cewa SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin INEC da rashin yin cikakken bayani kan sama da N126.46bn.

Ƙungiyar ta nemi kotu ta tilasta wa INEC bayyana yadda aka kashe kuɗin, waɗanda suka amfana da su da kuma kamfanonin da suka karɓi kwangiloli

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262