Zabe: Sule Lamido ya fita kunyar PDP da Atiku a mazabar sa

Zabe: Sule Lamido ya fita kunyar PDP da Atiku a mazabar sa

A jiya, Asabar, 23 ga watan Fabarairu ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majlisar tayya ('yan majalisar wakilai da dattijai) a fadin kasar nan.

Tun a jiyan sakamako su ka fara fitowa daga mazabu daban-daban da ke fadin kasar nan. Sai dai har yanzu hukumar zabe ta kasa (INEC) ba ta fara fitar da sakamako a hukumance ba.

Zaben dai ya fi jan hankali ne a matakin kujerar shugaban kasa tsakanin manyn ‘yan takara; shugaba Buhari a jam’iyyar APC da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP.

Manema labarai da ‘yan jarida sun fi mayar da hankali a kan sakamakon mazabun manyan ‘yan siyasa da ke goyon bayan ‘yan takarar biyu.

Zabe: Sule Lamido ya fita kunyar PDP da Atiku a mazabar sa
Sule Lamido
Asali: UGC

Wata majiyar mu daga jihar Jigawa ta sanar da mu cewar tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sule Lamido, ya fita kunyar jam’iyyar PDP da dukkan ‘yan takarar ta na kujerar hugaban kasa da na majalisar tarraya.

Tsohon gwamnan ya kada kuri’ar sa a mazabar sa ta Bamaina ‘C’ da ke garin Bamaina a karamar hukumar Birnin Kudu.

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya ke gudana a Sokoto, Jigawa da Kebbi

A matakin kujerar shugaban kasa jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 259 yayin da APC ta samu kuri’u 20.

Jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 278 a zaben kujerr dan takara Sanata yayin da APC ta samu 6. A matakin kujerar majalisar wakilai PDP ta samu kuri’u 267 yayin da APC ta samu 17.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel