Gaskiya Ta Fito bayan Shekaru 5, Kotu Ta Sallami Wanda Ake Zargi da Kashe Matarsa a Kano

Gaskiya Ta Fito bayan Shekaru 5, Kotu Ta Sallami Wanda Ake Zargi da Kashe Matarsa a Kano

  • Babbar Kotun Jihar Kano ta sallami tare da wanke Yusuf Nadabo Kawule daga zargin kashe matarsa bayan shekary biyar ana shari'a
  • Mai shari’a Nasir Saminu ya ce masu gabatar da ƙara sun kasa gabatar da isassun hujjoji don tabbatar da zargin
  • Lamarin ya faru ne a shekarar 2021 a ƙauyen Kogo da ke ƙaramar hukumar Takai ta jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Kano da ke zama Bompai ta sallami tare da wanke Yusuf Nadabo Kawule, wanda ake tuhuma da laifin kashe matarsa a wani lamari da ya faru a shekarar 2021.

Mai shari’a Nasir Saminu ne ya jagoranci shari’ar, inda ya yanke hukuncin cewa masu gabatar da ƙara sun kasa gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da zargin da ake yi wa mutumin.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta karɓi shaidu kan waɗanda ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki

Kotu.
Gudumar da masu shari'a ke amfani da ita a kotuna a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta ruwaito cewa hukuncin kotun ya biyo bayan sauraron shaidun da ɓangarorin biyu suka gabatar a lokacin shari’ar.

Hujjoji b su gamsarda kotu ba

Masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidunsu domin tabbatar da zargin da ake yi wa Yusuf, yayin da shi ma ya samu damar bayar da bayaninsa don kare kansa.

An tuhumi Yusuf da laifin kisan kai bisa sashe na 221 na kundin dokokin Penal Code. Sai dai ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

Bayan duba bayanan da aka gabatar a gaban kotu, Mai shari’a Saminu ya bayyana cewa hujjojin masu gabatar da ƙara ba su wadatar wajen tabbatar da zargin kisan kai ba.

Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin sallamar Yusuf tare da wanke shi daga tuhumar da ake yi masa.

Yadda lamarin ya faru

Lamarin da ya kai ga gurfanar da Yusuf a gaban kotu ya faru ne a shekarar 2021 a ƙauyen Kogo, da ke ƙaramar hukumar Takai ta Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano

A cewar bayanan da suka shafi shari’ar, ana zargin Yusuf da ɗaukar matarsa a kan babur domin zuwa wani ƙauye neman mata gida. A yayin tafiyar ne suka gamu da hatsari, wanda ya yi sanadin mutuwar matar.

Bayan faruwar hatsarin da mutuwar matar, jami’an tsaro sun kama Yusuf bisa zargin hannu a lamarin. Daga bisani, aka gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar tuhumar kisan kai.

CP Bakori
Kwamishinan rundunar yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori Hoto: Kano state police command
Source: Facebook

Kotu ta wanke magidancin

A lokacin shari’ar, an saurari shaidun masu gabatar da ƙara, sannan wanda ake tuhumar ya gabatar da bayaninsa domin kare kansa daga zargin.

A ƙarshe, kotun ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara ba su gabatar da hujjojin da suka isa su tabbatar da laifin da ake tuhumar Yusuf da shi ba.

Hakan ne ya sa Mai shari’a Nasir Saminu ya sallame shi tare da wanke shi daga tuhumar kisan matar tasa.

Kotu ta yi hukunci kan kisa Fatima

Kun ji cewa Babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Umar Auwalu mai shekara 23 da Yakubu Daiyebu mai shekara 21 hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An samu mutanen biyu da laifin kashe Fatima Abubakar mai shekara 35 da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi ranar 17 ga Janairu, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262