Zabe: Kotu ta bawa APC damar shiga zabe a Zamfara

Zabe: Kotu ta bawa APC damar shiga zabe a Zamfara

Wata kotun daukaka kara da ke jihar Sokot ta warware hukuncin da wata babbar kotu a jihar Zamfara ta yanke a kan hana hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) karbar sunayen ‘yan takarar jam’iyyar APC na kujeru daban-daban a zaben da za a yi cikin watan Fabarairu da Maris.

Hukuncin kotun ya share wa jam’iyyar APC hanyar shiga domin a fafata da ita a dukkan zabukan shekarar nan da za a fara ranar Asabar mai zuwa.

Kotun mai alkalai uku ta yi warware hukuncin kotun farkon ne biyo bayan janye karar da Aminu Jaji, wanda ya shigar, ya yi.

INEC ta kafe kan cewar ba zata karbi sunayen ‘yan takarar APC daga jihar Zamfara ba saboda gaza kammala zabukan cikin gida a kan lokaci da jam’iyyar ta yi.

Hukumar zaben ta tsaya tsayin daka a kan matakin da ta dauka bayan wasu hukunci ma su cin karo da juna da kotun jihar Zamfara da wata ta tarayya su ka zartar a rana guda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel