Arewa
Hatsarin mota a hanyar zuwa Minna ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 7 yayin da wasu suka ji raunuka. An bayyana lambobin motocin tare da adadin mutanen.
Hukumar jami'an dake tsaron gidan gyaran hali, wadda aka fi sani da ganduroba, ta bayyana gaskiyar lamari game da rahoton dake yawo kan Sheikh Abduljabbar.
Wani sarki a arewacin Najeriya ya ce ba zai yiwu Fulani makiyaya su ci gaba da lalata jiharsa ba, ya bukaci lallai su tattara su bar jihar cikin kwanaki 30.
Rundunar sojin Najeriya sun tabbatar da karbar wasu mayakan Boko Haram da suka mika wuya ga rundunar sojojin ta Najeriya. An bayyana adadin mayakan da aka karba
Gwamnan jihar Borno ya sanar da tallafin miliyoyin kudade ga sojojin da suka ji rauni a jiharsa yayin yaki da 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya a yankin.
Gwamnatin Najeriya ta yi nasarar kame Sunday Igboho, wani dan awaren Yarbawa da ya shahara a yankin kudu maso yammacin Najeriya tare da sukar gwamnati mai ci.
Masarautar Zazzau tabi sahun sauran masarautu a yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda ta sanar da soke hawa na babbar sallah (eid-el-kabir) saboda korona.
Wata babbar kotu a Abuja ta dakatar shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara daga mukaminsa saboda ya ki komawa jam'iyyar APC yayin da gwamna ya koma.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda sun hallaka wasu jami'an 'yan sanda a wani yankin jihar Zamfara. Rahoto ya bayyana yadda lamarin ya faru.
Arewa
Samu kari