Tsohon gwamnan Neja: Dole ne a ilmantar da 'yan Najeriya idan ana son bindiganci ya kare
- Tsohon gwamnan jihar Neja ya bayyana yadda matsalar jahilci ke kara ta'azzara rashin tsaro
- A cewarsa, matukar ba a ilmantar da 'yan Najeriya ba, to lallai ta'addanci ba zai kare ba a kasar
- Ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Neja, Mu'azu Babangida Aliyu, ya ce ba za a iya kawo karshen ta'addanci da tayar da kayar baya ba a Njierya idan har dimbin 'yan Najeriya ba su zama masu ilimi ba.
Aliyu ya bayyana haka ne yayin wani taro a Gidauniyar Sir Ahmadu Bello na Zauren Jagorancin shekarar 2021 da aka gudanar a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, karancin ilimin yadda za a ba da bayanai ga hukumomin ta hanyar al'ummomi kan masu aikata laifuka da ke ratsawa cikin yankunansu shi ya jawo rashin tattara bayanan sirri.
A kalamansa, cewa ya yi:
"Idan ba mu ilmantar da jama'armu ba, Boko Haram da sauran aikin ta'addanci ba zasu kare ba saboda za a samu mutane masu son yin fafutukar neman hakkinsu kuma suna ganin hakan daidai ne ta hanyar fada saboda kuna sanye da tufafi mafi kyau.
Aliyu, wanda kuma shine Shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar, ya ce tun lokacin da gidauniyar ta fara bayar da tallafin karatu ga marasa galihu a Arewa, ta ba da guraben karatu ga dalibai 800.
Boko Haram: Amurka ta fadi dalilin da yasa Najeriya ba za ta zama kamar Afghanistan ba
Kasar Amurka ta ba Najeriya tabbacin cewa maimaita abin da ya faru a Afganistan ba zai taba faru ba a Najeriya dake Afrika ta yamma, The Punch ta ruwaito.
Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard ce ta bayar da wannan tabbacin ranar Litinin 30 ga watan Agusta yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Jakadiyar ta yi bayanin cewa yanayin Najeriya da Afghanistan ba daya bane.
Wasu 'yan Najeriya sun gargadi Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) kan yiwuwar abin da ya faru a Afghanistan, inda 'yan Taliban suka mamaye kasar ya faru a Najeriya.
Amurka ta gama ficewa daga Afghanistan, jirgin karshe ya tashi ranar Litinin
A bangare guda, Hukumomin Amurka a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta sun sanar da cewa dukkan dakarunta sun fice daga kasar Afghanistan.
Jaridar Fox News ta ba da rahoton cewa jirgin C-117 na karshe dauke da membobin aiki na Amurka ya tashi daga filin jirgin saman Kabul da misalin karfe 3:29 na yamma agogon Amurka.
Fadar White House ta ce a cikin awanni 24 daga safiyar Lahadi, 29 ga Agusta zuwa Litinin, Amurka ta kwashe mutane 1,200 daga Kabul, tare da jiragen soji 26 da jiragen hadin gwiwa guda biyu dauke da wadanda suka fice daga kasar Afghanistan.
Asali: Legit.ng