Kafa jam'iyyar APC shine babban kuskuren da aka taba yi a Najeriya, inji Atiku
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki jam'iyyar APC mai mulki
- A cewarsa, APC itace babban kuskure da aka taba yi a Najeriya, kasancewar bata tabuka komai ba
- Ya kuma yi kira ga dandazon al'umma da su gaggauta komawa jam'iyyar adawa ta PDP
Adamawa - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin babban kuskuren Najeriya, Punch ta ruwaito.
Atiku wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar 4 ga watan Satumba a garin Yola, jihar Adamawa yayin taro da manyan jiga-jigan APC suka koma PDP, ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da APC.
Ya yi kira ga membobin APC da su barranta da jam'iyyar saboda abin da ya bayyana a matsayin muguwar rawar da ta taka, yana mai cewa sauya sheka daga jam'iyyar ya nuna alamar karshen APC.
Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki
Atiku ya ce:
“Mun yi babban kuskure a baya ta hanyar shawagi a wata jam’iyyar da ake kira APC. Amma daga yau ina kiran ku mutanen Adamawa da ku bar jam’iyyun ku ku koma PDP domin ita ce fatan talakawa, jam’iyya. APC ita ce babban kuskuren Najeriya.
“Jam’iyyar PDP ce ta raya Jihar Adamawa bayan APC ta kashe ta, ta shigar da jihar cikin halin ci gaban ababen more rayuwa.
“Yanzu makarantun mu sun fi kyau kuma cibiyoyin lafiyar mu suna cikin kyakkyawan yanayi. Ina addu’ar wannan taron zai zama farkon watsi da jam’iyyar APC.”
Taron ya samu halartar manyan tsoffin jiga-jigan APC
In ji rahoton Pulse, A yayin taron, fitattun tsoffin mambobin APC, ciki har da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Kobis Thimnu; Cif Daniel Bwala; Lambobin Sali; Umar Bello; Gwamna Ahmadu Fintiri sun tarbi Nedo Geofrey da Philip Gutuwa zuwa jam'iyyar PDP.
Da dumi-dumi: Shugaban APC da aka kora ya magantu kan sallamarsa daga jam'iyyar, yayi magana akan komawa PDP
Gwamnan ya tabbatar wa wadanda suka sauya shekar samar musu da adalci da kyautatawa.
Da yake nuna goyon baya ga tsayawa takarar shugaban kasa na Atiku, Fintiri ya bukaci masu ruwa da tsaki a PDP a jihar Adamawa da su yi aiki ba dare ba rana don habaka takararsa ga ‘yan Najeriya a wajen jihar ta Adamawa.
Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu
A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ba da shawarar kirkiro da sabuwar rundunar 'yan sanda don kare makarantu daga hare-haren 'yan bindiga a yankunan da lamarin tsaro yake kara ta'azzara.
Ya fadi hakan ne yayin da yake mayar da martani kan sace dalibai 73 da aka yi kwanan nan a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya dake Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Tsohon dan takarar shugaban kasan na jam'iyyar PDP ya kuma koka kan harin da sace daliban.
Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma
Asali: Legit.ng