Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

  • Wata kawar marigayi Abdulkarim Bala Na'Allah ta bayyana wasu abubuwan da suka faru kafin rasuwarsa
  • A cewarta, wasu tsageru sun kutsa gidan marigayin watanni biyu kafin 'yan ta'adda su hallaka shi
  • Ta bayyana wasu alherai da marigayin yake dashi bayan ta bayyana wasu maganganu da suka yi

Kaduna - Gidan da aka tsinci gawar Aldulkarim Bala Na'Allah a ranar Lahadi an ce a watanni biyu da suka gabata wasu tsageru sun afka gidan sun tafka sata a ciki, in ji rahoton Daily Trust.

Na’Allah, da gs Sanata Bala Ibn Na’Allah, mai wakiltar Kebbi ta kudu, an same shi daure yayin da wasu suka makure da igiya a ranar Lahadi a gidansa na Malali da ke Kaduna.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce maharan sun tsere da motarsa kirar Lexus SUV.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa
Abdulkarim Bala Na'Allah | Hoto: thecable/ng
Asali: UGC

Da aka zanta da kawar marigayin wacce take abokiyar karatunsa a Makarantar Sakandaren 'yan sanda ta Minna, ta tattaro cewa sun yi takaitaccen hira na kiran bidiyo a yammacin ranar Juma'a kafin matukin jirgin ya gaya mata cewa yana da taron gaggawa da zai halarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

“Na kira shi a mun yi hira ta bidiyo a ranar Juma’a da yamma amma yayin zantawarmu, tirela ta wuce don haka ban ji shi ba sai na gaya masa cewa zan sake kiransa daga baya.
“Daga nan sai ya sake kirana a wannan ranar da misalin karfe 6 na yamma da sakanni cikin tattaunawar mu, zan tambaye shi meke damunsa saboda fuskarsa ta nuna damuwa amma sai ya fada min cewa yana da taron gaggawa kuma zai tafi ofishin NEPA sannan zai kira ni daga baya.”

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

An tafka barna a gidansa watanni biyu da suka gabata

Ta ce wannan shi ne lokaci na karshe da ta ji daga gare shi amma ta shaida cewa watanni biyu da suka wuce, matukin jirgin ya sanar da ita cewa an yi wa gidansa fashi inda aka sace masa wasu na’urori.

Ta kara da cewa:

"An kutsa gidan, sun fasa katangar gidan suka shiga falo daga abin da ya gaya min kuma na shawarce shi da ya bar yankin tunda ba shi da kwanciyar hankali amma ya gaya min cewa an sada shi da mai gadi."

Kawar tasa ta makaranta, wacce ita ma mazauniyar garin Kaduna ce yayin da take kuka, ta shaida wa wakilin Daily Trust cewa:

“Ya ce wani ya yaudare shi kimanin Naira miliyan 50.
"Ya bai wa wani kudi don ya canza masa su zuwa dala amma mutumin ya yaudare shi. Mutumin ya biya shi N15m amma karar tana kotu a Kano har yanzu.”

Kara karanta wannan

Dokar hana fita na awanni 24: Mazauna Jos sun koka kan karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki

Ta bayyana marigayin a matsayin mutum mai tawali'u kana mai son cusa tarbiyya a tsakanin 'yan Najeriya.

Ta kara da cewa:

“Tazarar da ke tsakanin mu ba ta da yawa amma ya kasance yana min wasa yana cewa shi babana ne. Yana son mutane masu aiki tukuru wanda yana daya daga cikin dalilan da yasa muka shaku tun lokacin da muke makarantar sakandare.”

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

An gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali a jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa matukin jirgin mai shekaru 36, wanda ya yi aure kwanan nan, an daure shi kuma kana aka shake shi har ya mutu yayin da maharan suka tsere da motarsa ​​da kayayyakinsa.

Mai ba da shawara na musamman ga Sanata Na Allah, Garba Mohammed, yayin tabbatar da mummunan abin da ya faru, ya ce maharan sun samu shiga gidan ne ta rufin bayan gidansa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

A wani labarin, Sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata, PR Nigeria ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari.

An tsare daliban Islamiyyar na tsawon kwanaki 88 da awanni 11 gwargwadon lokacin da suka shafe a hannun 'yan bindigan kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel