'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

  • Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar cafke wani kasurgumin dan bindiga a jihar Kaduna
  • An tattaro cewa, dan bindigan dashi aka kitsa sace daliban Kwalejin Noma dake Afaka
  • Yayin da ake bincike, an gano wasu abubuwan ban takaici dangane munanan ayyukansa

Kaduna - Jami’an tsaro na rundunar ‘yan sanda sun cafke wani dan bindiga da ake zargin yana cikin ‘yan bindigan da suka afkawa Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Afaka da ke Jihar Kaduna a cikin watan Maris.

Daily Trust ta tattaro cewa wanda ake zargin yana daya daga cikin wadanda suka kitsa kuma suka kashe akalla mutane hudu da suka sace daga cikin dalibai 37 na kwalejin a ranar 11 ga Maris 2021.

An saki daliban bayan kwanaki 55 da aka yi garkuwa da su kuma an biya kimanin Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Sai dai wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaro sun afkawa al’ummar Askolaye da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu a ranar Lahadin da ta gabata bayan sun bi diddigin wanda ake zargin na tsawon makwanni.

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka
Jami'an 'yan sanda | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin unguwar wanda ya shaida faruwar lamarin ya ce wanda ake zargin ya zo unguwar kusan watanni biyu da suka gabata kuma ya yi hayar gida da nufin shigar da 'ya'yansa na riko guda biyu a makarantar Islamiyya.

Ya shaida cewa jami’an tsaro sun tsare wanda ake zargi da matarsa ​​yayin da aka saki shugabannin al’umma da makwabtan da aka gayyata don yin tambayoyi.

Wani mazaunin garin ya shaida cewa matar da ake zargi, wacce mahaifinta da mijinta, ’yan bindiga suka kashe ba ta san mijinta na yanzu tsagera bane kuma shi ne ya jagoranci aikin da ya kai ga kashe mahaifinta da mijinta.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Dagajin Ƙauyen Bororo Sun Kashe Shi a Kwara

A cewar majiyar:

“Bayan ya kashe mijinta, ya dawo ya aure ta sannan ya dauki 'ya’yanta duka wadanda ba sAu wuce shekara bakwai ba.
"Ba ta san duk wannan ba har sai da aka kama shi kuma ya furta gabanta yayin tambayoyi. Ya kuma furta cewa yana cikin wadanda suke kashe-kashe da sace-sacen 'yan makaranta da dama ciki har da na daliban Afaka.".

Wani mazaunin garin da ya yi mu'amala da wanda ake zargin ya shaida cewa ya yi ikirarin ya fito ne daga Ilorin, jihar Kwara, kuma ya zo da iyalansa don yi musu rajista a makaranta.

Ya ce:

“Ya gaya mana cewa sunansa Abubakar, ba mu sani ba ko wannan shi ne ainihin sunansa, amma abokinsa wani tela da ke zaune a Badarawa ne ya gabatar mana dashi.
"Amma abokin nasa tela ya gaya wa jami’an tsaro cewa alakarsa da wanda ake zargi ta dogara ne kan yadudduka da yake kawo masa don dinki saboda bai san cewa wanda ake zargin yana cikin 'yan bindiga ba.”

Kara karanta wannan

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

Da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta hannun jami’in hulda da jama’a, ASP Mohammed Jalige, ya ki bayar da cikakken bayani kan kamun amma ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

Garin kai hari, 'yan sanda suka samu nasarar harbe shugaban 'yan bindiga a jihar Neja

Jami’an rundunar da ke yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Najeriya, tare da tallafin 'yan banga, a ranar Litinin 30 ga watan Agusta sun hallaka wani sanannen shugaban ‘yan bindiga, Jauro Daji, a jihar Neja.

Sun kuma kashe wasu 'yan bindiga da yawa yara ga Daji a yankin Kontagora na jihar. An kuma kwato babura goma daga hannun 'yan bindigar.

A cewar majiyar, rundunar 'yan sandan ta yi aiki da sahihan bayanan sirri kuma ta yi wa 'yan bindigan kwanton bauna, inda suka kashe Daji, tare da yaransa, wadanda ke kokarin tsallaka wani rafi a cikin daji, don yin garkuwa da mutane a wani gari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu

Da yake zantawa da PRNigeria, daya daga cikin majiyoyin, wani jami’in leken asiri ya ce:

“Hadin gwiwar 'yan sanda da ‘yan banga na yankin ne suka kashe Jauro Daji tare da kashe 'yan bindigan dake shirin yin garkuwa da mutanen da basu ji ba basu gani ba a wani kauye.
“Shahararre Jauro Daji wanda ake zargin yana da hannu a hare-haren da aka kai kauyuka da makarantu ya jagoranci sauran 'yan bindigan masu yawa akan babura."

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A wani labarin, Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ce za su bibiyi duk wani mutumin da ya kai hari kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kuma su kama su don fuskantar fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma ce za su cafke mazauna unguwar ko yankin da abin ya faru don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargi suka tsere.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai a ranar 14 ga watan Agusta a kusa da hanyar Gada-biyu-Rukuba na karamar hukumar Jos ta Arewa da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel