Sanata Wammako ya nada mataimaka na musamman 18 a mazabarsa a rana daya

Sanata Wammako ya nada mataimaka na musamman 18 a mazabarsa a rana daya

  • Sanata Aliyu Wammako ya nada mataimaka na musamman 18 a mazabarsa ta jihar Sokoto
  • A cewarsa, nade-naden zai taimaka masa wajen isar da romon dimokradiyya a yankunansa
  • Ya kuma bukacesu da asu kasance masu riko da gaskiya da amana wajen gudanar da ayyukansu

Sokoto - Sanata Aliyu Wamakko (APC-Sokoto) ya nada sabbin mataimaka na musamman guda 18 (SAs) don saukaka isar da romon dimokuradiyya ga mazabarsa.

Wamakko, wanda ke wakiltar gundumar Sanatan Sokoto ta Arewa, ya kasance tsohon gwamnan jihar Sokoto.

Ya ce sabbin nade-naden na nufin kara rage rashin aikin yi a jihar, PM News ta ruwaito.

Sanata Wammako ya nada mataimaka na musamman 18 saboda gamsar da mazabarsa
Sanata Aliyu Wammako | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wamakko ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

“Wadannan sabbin da aka nada sun kasance ko dai tsoffin Shugabanin Kananan Hukumomi, Sakatarori ko tsoffin 'yan majalisa, da sauran manyan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da sauransu.
“Wannan ishara kuma za ta kara karfafa ayyukana na majalisa a Majalisar Tarayya da nufin tabbatar da ingantaccen wakilci sa mazabata.

Ya kuma kara ba da tabbacin cewa, nan gaba zai sake nada sabbin mataimaka na musamman a yankin nasa.

Wamakko, wanda ke jagorantar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, ya bukaci sabbin mataimakan da su rike amana da amincewar da aka yi masu saboda nadin nasu ya ginu ne bisa cancanta.

Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18

Watannin baya a jihar Kano, wani kansila a jihar Kano ya yi abin da ba a saba gani ba ta hanyar nada mutum 18 wadanda za su yi aiki tare da shi wajen gudanar da ayyukan da aka dora masa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: IGP Baba ya bayyana yadda ya zama shugaban yan sanda a mawuyacin lokaci

Kansilan, Hon Muslihu Yusuf Ali, mai wakiltar unguwar Guringawa na karamar hukumar Kumbotso, ya kaddamar da hadiman 18 a sakateriyar karamar hukumar a ranar Alhamis tare da taimakon Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Shamsu Abdullahi.

Da yake zantawa da Daily Trust bayan an rantsar da shi, Hon Ali ya ce a kullum burinsa shi ne ya kawo canje-canje idan ya samu dama; damawa da kowa tare da aiki da ci gaban jama'arsa.

Hon Ali ya ce, a matsayinsa na shugaba, akwai bukatar ya nada ko da hadimai sama da 18 ne domin su taimaka masa da kuma bayar da rahoton abin da mutane suke bukata daga tushe wanda a cewarsa, shugabanni da yawa ba sa damuwa da yi.

Kafa jam'iyyar APC shine babban kuskuren da aka taba yi a Najeriya, inji Atiku

A wani labarin kuwa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin babban kuskuren Najeriya, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jihar Bauchi: Gwamna Bala Mohammed ya rantsar da sabbin kwamishinoni

Atiku wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar 4 ga watan Satumba a garin Yola, jihar Adamawa yayin taro da manyan jiga-jigan APC suka koma PDP, ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da APC.

Ya yi kira ga membobin APC da su barranta da jam'iyyar saboda abin da ya bayyana a matsayin muguwar rawar da ta taka, yana mai cewa sauya sheka daga jam'iyyar ya nuna alamar karshen APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel