Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bada umarnin kame malamai masu wa'azin tunzura jama'a
- Gwamnan ya bukaci hukumar DSS da su gaggauta cafke irin wadannan malamai masu ta da hankalin jama'a
- Ya kuma bukaci kungiyoyin addinai da su nemi izinin wa'azi daga gwamnatin jihar kafin gudanar da hakan
Borno - Jaridar Punch ta rahoto cewa, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umarci jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su kamo duk wani malamin da ke wa’azi a fili tare da tunzura jama’a kan junan su.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a taron tattaunawa kan yanayin tsaro na jihar wanda ya samo asali daga mika wuya na daruruwan mayakan Boko Haram a gidan gwamnati ranar Lahadi a Maiduguri.
A cewar gwamnan:
“Wani muhimmin abu da nake son tattaunawa anan shine batun wa’azi a jihar. Idan ba a kula ba, wannan zai zama babban lamari saboda na ji masu wa'azi daban-daban sun fara cin zarafin juna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na ji suna cin zarafin juna a wa’azin su. Na umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kamo dukkaninsu a jihar. An bai wa Hukumar Hidimar Wa’azi dukkan ikon da za ta tsara ayyukansu.
“Ba za mu taba yarda wani ya shigo jihar ya fara fadin munanan kalamai ba, Kirista ne ko Musulmi.
"Wannan yana da matukar muhimmanci. Yakamata kungiyar CAN ta rubuta mana, Jama’atu Nasri Islam suma su rubutawa gwamnatin jihar Borno da hukumar hidimar wa’azi da nufin samar musu da damar yin wa’azi. Wannan yana da matukar mahimmanci."
Kashi 10 na jama'ar Borno sun bace saboda Boko Haram, inji Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana cewa ba a san inda akalla 10% cikin 100% na al'ummar jihar suke ba sakamakon rikicin 'yan ta'adda a jihar, The Nation ta ruwaito.
Zulum, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar gwamnati bayan wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, ya kuma ce an kashe mutane sama da 100,000 a cikin shekaru 12 da suka gabata na rikicin Boko Haram.
Gwamnan, wanda ya ce ya tattauna rahoton mika wuya da mayakan Boko Haram suka yi da Shugaban kasa, ya kara da cewa bai ga dalilin da zai sa a ki amincewa da wadanda suka mika wuya ba.
Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon da mutum 50, sun hallaka mutum 4 a Maradun
A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Litinin 23 ga watan Agusta ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka mutum hudu tare da yin awon gaba da wasu mutum 50 a garin Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Muhammad Shehu, ya ce maharan, wadanda suka zo da yawansu, sun mamaye garin da tsakar daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu tare da sace wasu 50.
Asali: Legit.ng