Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina
- Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun cafke wasu tubabbun 'yan bindiga da suka koma ruwa
- Rahoto ya bayyana cewa, an cafke su ne yayin da suka kai farmaki kan wani makiyayi a jihar ta Katsina
- A halin yanzu sun amsa laifinsu, kuma za a gurfanar dasu a gaban kotu nan ba da jimawa ba inji 'yan sanda
Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Laraba 1 ga watan Satumba ta gabatar da mutane 12 da ake zargi ciki har da tubabbun 'yan bindiga guda uku bisa laifuka daban-daban da suka hada da fashi, satar shanu da garkuwa da mutane.
Tubabbun 'yan bindigan su ne Abdullahi Mai-Rafi mai shekaru 43; Abbas Haruna mai shekaru 34; da Usman Hassan mai shekaru 50, jaridar Punch ta ruwaito.
Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Katsina, cewa ana zargin mutanen uku sun kai hari kan wani makiyayi, Alhaji Gide Suleiman, a ranar 11 ga Agusta, 2021, a dajin Dammarke a karamar hukumar Ingawa.
Ya ce mutanen sun sace shanu 20 da darajarsu ta kai N7.5m daga wurinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ana zargin wadanda ake zargin sun saci N40,000 da wayoyin hannu hudu daga mutumin da suka yi wa barna.
Rahoto ya ce an riske su a ranar 24 ga Agusta, 2021, lokacin da ake zargin sun sake kai wani farmakin.
Sun so su sace wasu shanun daga gare shi lokacin da 'yan sanda suka cafke su.
Isah ya ce an kwato shanu biyu da kudi N444,000.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin su kuma nan ba da jimawa ba za su gurfana a gaban kotu.
Garin kai hari, 'yan sanda suka samu nasarar harbe shugaban 'yan bindiga a jihar Neja
Jami’an rundunar da ke yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Najeriya, tare da tallafin 'yan banga, a ranar Litinin 30 ga watan Agusta sun hallaka wani sanannen shugaban ‘yan bindiga, Jauro Daji, a jihar Neja.
Sun kuma kashe wasu 'yan bindiga da yawa yara ga Daji a yankin Kontagora na jihar. An kuma kwato babura goma daga hannun 'yan bindigar.
A cewar majiyar, rundunar 'yan sandan ta yi aiki da sahihan bayanan sirri kuma ta yi wa 'yan bindigan kwanton bauna, inda suka kashe Daji, tare da yaransa, wadanda ke kokarin tsallaka wani rafi a cikin daji, don yin garkuwa da mutane a wani gari.
Da yake zantawa da PRNigeria, daya daga cikin majiyoyin, wani jami’in leken asiri ya ce:
“Hadin gwiwar 'yan sanda da ‘yan banga na yankin ne suka kashe Jauro Daji tare da kashe 'yan bindigan dake shirin yin garkuwa da mutanen da basu ji ba basu gani ba a wani kauye.
“Shahararre Jauro Daji wanda ake zargin yana da hannu a hare-haren da aka kai kauyuka da makarantu ya jagoranci sauran 'yan bindigan masu yawa akan babura.
“An yi nasarar aiwatar da aikin a ranar Litinin tsakanin Gulbin Boka zuwa yankin Dogon Fadama a karkashin karamar hukumar Kontagora. Mun kuma kwato babura goma.
"Mun dauki kwararrun masu iyo domin gano makaman wasu daga cikin 'yan bindigan da suka tsere da gawawwakinsu da aka jefa cikin kogi."
'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka
A wani labarin, Jami’an tsaro na rundunar ‘yan sanda sun cafke wani dan bindiga da ake zargin yana cikin ‘yan bindigan da suka afkawa Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Afaka da ke Jihar Kaduna a cikin watan Maris.
Daily Trust ta tattaro cewa wanda ake zargin yana daya daga cikin wadanda suka kitsa kuma suka kashe akalla mutane hudu da suka sace daga cikin dalibai 37 na kwalejin a ranar 11 ga Maris 2021.
An saki daliban bayan kwanaki 55 da aka yi garkuwa da su kuma an biya kimanin Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaro sun afkawa al’ummar Askolaye da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu a ranar Lahadin da ta gabata bayan sun bi diddigin wanda ake zargin na tsawon makwanni.
Asali: Legit.ng