IBB Ya Fadi Wadanda ke Taimakawa Juyin Mulki ke Yin Nasara a Najeriya

IBB Ya Fadi Wadanda ke Taimakawa Juyin Mulki ke Yin Nasara a Najeriya

  • Tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi magana game da yadda ake yin nasara a juyin mulki
  • IBB ya ce attajirai sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa da daukar nauyin juyin mulkin soja a lokuta daban-daban cikin tarihin Najeriya
  • Ya kuma bayyana yadda aka samu zargin Mamman Vatsa da hannu cikin yunkurin juyin mulkin shekarar 1985

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana yadda ake samun nasara a juyin mulki.

IBB ya ce babu wani juyin mulkin soja da ya yi nasara a tarihin kasar ba tare da sa hannun ko goyon bayan fararen hula ba.

IBB ya yi magana kan yadda ake nasara a juyi mulki
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida. Hoto: @aonanuga1956.
Source: Twitter

Jaridar THISDAY ta ruwaito cewa Babangida, wanda zai cika shekaru 85 a ranar Litinin, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan rediyon Badeggi 90.1 FM da ke Minna, Niger.

Kara karanta wannan

Yayin da bincike ke ƙara zurfi, tsohon gwamna ya magantu kan zargin juyin mulki

‘Yadda Fararen hula ke tallafawa juyin mulki’

Babangida ya ce attajirai sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa da daukar nauyin juyin mulkin soja a lokuta daban-daban cikin tarihin Najeriya.

Ya ce:

“Babu wani juyin mulkin da ya yi nasara a tarihin Najeriya da ya faru ba tare da sa hannun fararen hula ba.”

Tsohon shugaban mulkin sojan ya kuma tuna abubuwan da suka faru a lokacin yunkurin kifar da gwamnatinsa a shekarar 1985, da kuma kisan Mamman Vatsa, wanda a lokacin shi ne ministan Abuja.

Babangida ya ce Vatsa, wanda ya bayyana a matsayin abokin karatunsa kuma makusancinsa, ya fara musanta hannu cikin wannan yunkurin juyin mulkin.

Ya ce da farko ya yi wahalar yarda da zargin da ake dangantawa Vatsa da shirin juyin mulkin, saboda dadewar abokantakarsu da tarihin da suka yi tare.

IBB ya magantu kan yadda ake nasara a juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu ya yi tagumi a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yadda IBB ya gana da Batsa, Nasko

Babangida ya ce ya gayyaci Vatsa da Mohammed Gado Nasko zuwa ofishinsa bayan wani babban jami’in soja ya sanar da shi cewa an ambaci sunayensu cikin shirin kifar da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Duka bayanan da suka fito daga juyin mulkin da aka yi yunkurin yi wa Tinubu

Ya ce lokacin da suka isa ofishinsa, ya tambaye su game da rahotannin da ke cewa an ambace su cikin shirin juyin mulkin, amma dukansu sun musanta hannu a lamarin.

Daga bisani, an kafa kwamitin binciken soji domin gudanar da bincike kan zarge-zargen, cewar TheCable.

IBB ya ce yayin da aka wanke Janar Gado Nasko daga duk wani laifi, kwamitin ya gano hujjojin da ke danganta Vatsa da shirin juyin mulkin.

Ya ce ya ji “mamaki, takaici da kuma matukar bakin ciki” bayan da aka tabbatar da hannu Vatsa cikin lamarin.

Babangida ya ce babu abin da zai iya yi domin kare Vatsa daga hukuncin da dokar soja ta tanada.

IBB ya magantu kan matsalolin Arewa

A baya, an ji cewa tsohon shugaban kasa, ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana game da rashin tsaro da talauci a Arewa.

IBB da Janar Alani Akinrinade mai ritaya sun koka cewa Najeriya ta rasa shugabanni masu ɗabi’a, gaskiya da kishin ƙasa.

Suka ce dabi'u irin na marigayi Janar Hassan Katsina shi ne abin da ya kamata kowa ya yi koyi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.