Rikicin Jos: Gwamnatin Plateau ta sassauta dokar hana fita a wasu sassan jihar

Rikicin Jos: Gwamnatin Plateau ta sassauta dokar hana fita a wasu sassan jihar

  • Gwamnan jihar Filato ya sassauta dokar hana fita a wasu yankunan jihar bayan kwanaki
  • A bayan an sanya dokar hana fita a wasu sassa uku na jihar Filato bayan barkewar rikici
  • Gwamnan ya lissafo yadda sassaucin dokar hana fitan za ta kasance a yankunan uku

Plateau - Gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana fita da aka kafa a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta Kudu da Bassa, inji Daily Trust.

Gwamna Simon Lalong ya sanya dokar hana fita ne bayan tashin hankalin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama, kona gidaje da barnata dukiyar al'umma.

An kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin Jos ta Arewa (inda aka fi samun tashin hankali), yayin da Jos ta Kudu da Bassa aka sanya dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Kara karanta wannan

Dokar hana fita na awanni 24: Mazauna Jos sun koka kan karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Plateau ta sassauta dokar ta hana fita a wasu sassan jihar
Gwamnan jihar Filato | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Dokar hana fitan ta kasance tana aiki har zuwa safiyar yau Litinin 30 ga watan Agusta lokacin da gwamnan jihar ya sake sassauta ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lalong ya ce an sassauta dokar hana fita a Jos ta Arewa daga awanni 24 zuwa daga 6 na yamma zuwa 6 na safe, yayin da a Bassa da Jos ta Kudu wanda tun farko karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe yanzu zai kasance daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Batun zirga-zirga a yankunan

“Dokar hana yawo da a daidaita sahu (Keke NAPEP) da masu talla za ta ci gaba da aiki a cikin garin Jos/Bukuru, kuma taron tattalin arziki da saka hannun jari na Filato da aka shirya yi a ranar 1 da 2 ga Satumba 2021 an dage ranarsa. Za a sanar da sabon kwanan wata da kuma sanar da duk masu gayyatar mu."

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an hukunta duk mutanen da aka samu da hannu dangane da hare-haren da aka kai kwanan nan a jihar Filato, The Cable ta ruwaito.

An kai hare-hare kan mutane da dama a garin Jos, babban birnin jihar Filato, da sauran sassan kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda ya yi sanadiyar kashe-kashen mutane da dama, yayin da wasu mazauna garin da dama suka samu raunuka.

Sakamakon hare-haren da aka kai a Jos wasu gwamnatocin jihohi sun kwashe 'yan asalin jihohinsu dake karatu daga jihar ta Filato.

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

A baya kun ji cewa, an gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi barazanar hukunta jami'an da aka samu da cin amana

Daily Trust ta tattaro cewa matukin jirgin mai shekaru 36, wanda ya yi aure kwanan nan, an daure shi kuma kana aka shake shi har ya mutu yayin da maharan suka tsere da motarsa ​​da kayayyakinsa.

Mai ba da shawara na musamman ga Sanata Na Allah, Garba Mohammed, yayin tabbatar da mummunan abin da ya faru, ya ce maharan sun samu shiga gidan ne ta rufin bayan gidansa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel