'Yan ISWAP sun fatattaki mazauna daga gidajensu a jihar Borno zuwa kasar Kamaru

'Yan ISWAP sun fatattaki mazauna daga gidajensu a jihar Borno zuwa kasar Kamaru

  • Mambobin kungiyar ISWAP sun kai hari wani yankin jihar Borno, sun fatattaki mazauna yankin
  • Rahoto ya bayyana cewa, 'yan ISWAP din sun kone gidaje kuma sun yi artabu da sojoji a yankin
  • Duk da babu cikakken bayani game da rahoton, amma an ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun bar mazauna yankin sun tafi ba tare sun taba su ba

Borno - Kungiyar ISWAP ta kaddamar da wani gagarumin sabon hari a Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Bayanai sun ce mazauna garin da yawa sun tsere zuwa Kamaru sakamakon wannan harin.

Rann gari ne a jihar Borno dake da iyaka da kasar Kamaru.

Da dumi-dumi: ISWAP sun fatattaki wasu mazauna daga gidajensu a jihar Borno
'Yan ta'addan ISWAP | Hoto: arewaagenda.com
Asali: UGC

An ce mayakan dauke da muggan makamai sun kutsa cikin garin da sanyin safiyar Litinin 30 ga watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Dokar hana fita na awanni 24: Mazauna Jos sun koka kan karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki

Har yanzu ba a samu wasu cikakkun bayanai game da harin ba, amma an ba da rahoton sun kona gidaje da yawa tare da yin artabu da musayar wuta da sojoji.

Wani mazaunin garin ya ce maharan sun kyale fararen hula su bar garin ba tare da wani rauni ba.

Wata majiyar kuma ta ce mayakan na ISWAP sun tsere daga garin bayan da sojoji suka fi karfinsu.

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

A bangare guda a jihar, jaridar Punch ta rahoto cewa, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umarci jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su kamo duk wani malamin da ke wa’azi a fili tare da tunzura jama’a kan junan su.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist

Gwamnan, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a taron tattaunawa kan yanayin tsaro na jihar wanda ya samo asali daga mika wuya na daruruwan mayakan Boko Haram a gidan gwamnati ranar Lahadi a Maiduguri.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon da mutum 50, sun hallaka mutum 4 a Maradun

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Litinin 23 ga watan Agusta ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka mutum hudu tare da yin awon gaba da wasu mutum 50 a garin Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhammad Shehu, ya ce maharan, wadanda suka zo da yawansu, sun mamaye garin da tsakar daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu tare da sace wasu 50.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu matan aure a Zariya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel