Aisha Buhari
Wata mace 'yar Najeriya, Bolouere Opukiri ta rasa aikin ta mako daya bayan ta yi suka a kan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha a dandalin sada zumunta na Twitter.
Wani babban Lauyan Duniya mai rajin kare hakkin Jama'a ya soki Shugaba Buhari. Babban Lauyan yayi tir da yadda ake yakar ta’addanci a Kasar inda yace akwai son zuciya da nuna banbancin addini wajen Shugaba Muhammadu Buhari.
A ranar Talata 15 ga watan Mayu ne shuwagabannin kungiyar matan Arewa suka kai ma uwargidar shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, Aisha Buhari a fadar Villa dake babban birnin tarayya Abuja.Labari cikin hotuna
Za kuji abubuwa 5 da Simon Kolawole ya rubuta a budaddiyar wasikar sa ga Shugaba Buhari. Wannan fitaccen ‘Dan jarida ya fadawa kasa Buhari cewa akwai gyara a Gwamnatin sa. Dama dai an ce gyara kayan ka ba sauke mu raba ba.
Matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta bukaci cibiyoyin kiwon lafiya na kudi a Najeriya da su rangwanta kudin da suke karba don aikin su a kasar. Matar shugaban tayi Kiran ne a lokacin da kungiyar likitocin gwamnati da masu zaman...
Oladope Agoro yace Shugaba Buhari ya koma gona kurum. Wasu su na ganin Baba Buhari ya gaza don haka ya koma gida ya huta a 2019. Agoro yace Mai dakin Shugaban kasa Aisha Buhari za ta zama Mataimakiyar sa a takarar zaben 2019
Gobe Asabar 17 ga watan Fabrairu zaiyi daidai da zagayowar ranar haihuwar Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha. Aisha ta kasance mata ga shugaban kasa Buhari tun bayan rabuwarsa da matarsa ta farko marigayiya.
Senata mai wakiltar mazabar Kudancin jihar Bayelsa, Ben Murray-Bruce, yace, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari mace ce mai basira da za ta iya shugabanci da kyau Senata ya bayyana haka ne a shafin sa na tuwita a ranar Juama'a
Rahoto daga mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara, Bashir Ahmed ya nuna cewa na sallami Yusuf Buhari daga Asibiti. Dan shugaba Buharin dai ya samu hadari ne sanadiyar wasa da babur tare da wani abokinsa a cikin garin Abuja
Aisha Buhari
Samu kari