Matasan Tinubu Sun Gaji da Kame Kame, Sun Kama Layin Atiku saboda Zaɓen 2027

Matasan Tinubu Sun Gaji da Kame Kame, Sun Kama Layin Atiku saboda Zaɓen 2027

  • Wata kungiyar matasa a Arewa mai suna Tinubu Northern Youth Forum ta janye goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu, inda ta koma bayan Atiku Abubakar
  • Kungiyar ta sauya sunanta zuwa Arewa Youth For Atiku (AYA), domin fadada harkokin wayar da kan jama'a da shiga harkokin siyasa a yankin Arewa
  • Ta sanar da shirin sauya sheka zuwa ADC tare da bayyana goyon bayanta ga Atiku a wani taro da aka shirya gudanarwa a Azare, jihar Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Bauchi - Kungiyar matasan da a baya ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ta sanar da janye goyon bayanta ga shugaban kasar, inda ta bayyana komawa bayan Atiku Abubakar, gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kungiyar ta kuma sauya sunanta daga Tinubu Northern Youth Forum zuwa Arewa Youth For Atiku (AYA), a wani mataki na sauya alkiblar siyasarta da kuma fadada ayyukanta a yankin Arewa.

Wasu magoya bayan Tinubu sun koma bayan Atiku
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata takarda da Adamu Jikan Manu ya sanya wa hannu a madadin kungiyar a ranar 13 ga watan Nuwambar 2026, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya samu tagomashi yayin da Tinubu ya gamu da koma baya a Arewa

Kungiyar ta shirya shiga ADC

A cewar sanarwar, kungiyar ta shirya gudanar da bikin bayyana goyon bayanta ga Atiku Abubakar tare da sanar da komawarta jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).

An shirya gudanar da taron ne a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, a ofishin dabarun siyasa na jam'iyyar ADC da ke Azare, jihar Bauchi.

Mai shirya taron kuma jagoran kungiyar, Hon. Auwal Ibrahim Sansani, CNA, ne zai jagoranci bikin domin tabbatar da nasarar Atiku.

Dalilin sauya sunan kungiyar

Kungiyar ta bayyana cewa sauya sunanta zuwa Arewa Youth For Atiku Abubakar wani yunkuri ne na samar da babbar kafa da za ta hada matasa wajen wayar da kan jama'a, fadada hulda da al'umma da kuma karfafa shigar jama'a cikin harkokin dimokuradiyya a fadin Arewacin Najeriya.

Ta kuma yi kira ga mambobinta, magoya baya, shugabannin al'umma da na addini, kungiyoyin mata da matasa, dalibai, 'yan kasuwa da kwararru da su halarci taron bayyana matsayinta.

Kara karanta wannan

Sanata ya faɗawa Hausawa Kiristoci amfanin zaɓen Tinubu a 2027

Kungiyar ta yi kira ga 'yan Najeriya

A cikin sanarwar, kungiyar ta ce tana ganin Najeriya na bukatar shugabanci nagari, hadin kan kasa, ingantaccen mulki da kuma bai wa 'yan kasa damar taka rawa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

Ta bukaci 'yan Najeriya masu ra'ayi irin nata da su shiga yakin neman goyon bayan Atiku, tare da tabbatar da zaman lafiya da bin ka'idojin dimokuradiyya gabanin babban zaben 2027, cewar Vanguard.

Kungiyar ta kammala sanarwarta da taken:

"Ku shiga tafiyar Atiku. Ku zabi Atiku domin ceto Najeriya daga halin da kasar ke ciki."

Kalubalen da ke gaban Atiku, ADC

Mun ba ku labarin cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da rusa matakan da kwamitin ya ɗauka.

Hukuncin ya jefa takarar Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi cikin barazanar shari’a, duk da cewa jam’iyyar mai adawap ta ɗaukaka ƙara.

Idan kotunan ɗaukaka ƙara da Kotun Ƙoli suka tabbatar da hukuncin, Atiku na iya rasa damar tsayawa takara, lamarin da zai iya sauya lissafin siyasar adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.