Baya goya marayu: Uwargidar gwamnan jahar Borno ta gina ma marayu wata katafariyar makaranta

Baya goya marayu: Uwargidar gwamnan jahar Borno ta gina ma marayu wata katafariyar makaranta

Uwargidar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta kai ziyara jahar Borno inda ta kaddamar da wata katafariyar makaranta ta zamani da uwargidar gwamnan jahar Borno, Nana Kashim Shettima ta gina ma marayu.

Legit.com ta ruwaito a ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba ne Aisha ta kaddamar da wadannan makarantu wanda uwargidar gwamnan jahar Borno Kashim Shettima, Nana, ta gina ma marayu, yayan Fulani da aka kashe iyayensu.

Baya goya marayu: Uwargidar gwamnan jahar Borno ta gina ma marayu wata katafariyar makaranta
Aisha da Nana
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kallo ya koma sama: An tafka sata a majalisun dokokin Najeriya

Bugu da kari, uwargidar shugaba Buhari, Aisha, ta kaddamar da wasu rukunin azuzuwa da aka ginasu a gidan sama mai hawa daya a wata makarantar sakandari ta mata dake garin Maiduguri na jahar Borno, inda ta tattauna da daliban.

Da take gabatar da jawabinta, Aisha ta jinjina ma uwargidar gwamnan jahar Borno, Nana Shettima da kuma gwamnatin jahar Borno a karkashin jagorancin Gwamna Kashim bisa jagoranci na gari da yake gudanarwa a jahar.

Baya goya marayu: Uwargidar gwamnan jahar Borno ta gina ma marayu wata katafariyar makaranta
Makaranta
Asali: Facebook

“Duk ayyukan nan dana zagayasu a yau sun tabbatar da kokarin da gwamnatin jahar Borno keyi na samar da ayyukan cigaba a kusan shekaru takwas da tayi duk da matsalar hare haren kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.” Inji ta.

Haka zalika Aisha ta leka makarantar marayu da take ginawa a karkashin gidauniyarta ta Future Assured a Maiduguri, don ganin matsayin da aikin ya kai zuwa yanzu, a yayin ziyarar Aisha ta bayyana cewa zata kammala aikin makarantar zuwa shekara mai zuwa.

Baya goya marayu: Uwargidar gwamnan jahar Borno ta gina ma marayu wata katafariyar makaranta
Makaranta
Asali: Facebook

Daga karshe gwamnatin jahar Borno ta karrama Aisha Buhari da lambar yabo bisa kokarin da take yi tare da jajircewar da take nunawa wajen taimaka mata da kananan yara ta hanyar tallafin kiwon lafiya da ilimi da take basu.

Baya goya marayu: Uwargidar gwamnan jahar Borno ta gina ma marayu wata katafariyar makaranta
Makaranta
Asali: Facebook

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel