'An Jikkata Mutane da Dama a Harin da aka kai wa Kwankwaso a Kano,' Obi
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Bichi, jihar Kano
- A bayanan da ya yi, Peter Obi ya ce mutane da dama sun jikkata, yayin da aka lalata motoci kusan bakwai a yayin harin
- Ya bukaci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa tare da kama wadanda suka kai harin da wadanda suka dauki nauyinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi magana kan harin da aka kai wa ayarin motocin abokin takararsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a karamar hukumar Bichi da ke jihar Kano.
Obi ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya bukaci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gaggauta gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Source: Facebook
Abin da Peter Obi ya ce kan harin
A cikin wata sanarwa da ya fitar a X, Obi ya ce ya samu bakin ciki matuka bayan samun rahoton harin da aka kai wa ayarin motocin Kwankwaso da mutanen da ke tare da shi.
Ya bayyana cewa rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun samu raunuka, yayin da aka lalata motoci kusan bakwai.
Obi ya ce bai kamata a bar tashin hankali ya zama wani bangare na siyasar Najeriya ba, yana mai cewa bambancin ra’ayin siyasa ba dalili ba ne na kai hari ko lalata dukiyoyin jama’a.
Ya kara da cewa kowane dan Najeriya na da hakkin shiga harkokin dimokuradiyya ba tare da fargabar fuskantar barazana ba.
Obi ya bukaci a yi bincike
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi kira ga rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su fara bincike cikin gaggawa domin gano wadanda suka kai harin.
Ya kuma bukaci a gano duk wanda aka samu da hannu wajen daukar nauyin harin, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da su gaban kuliya.
Obi ya jaddada cewa babu wani mutum da ya fi karfin doka, ko da kuwa matsayinsa na siyasa ko tasirinsa a cikin al’umma.
Ya kuma bayyana goyon bayansa ga Kwankwaso, shugabannin NDC na jihar Kano da duk wadanda harin ya shafa, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Source: Twitter
Obi ya ce dimokuradiyya ba yaki ba ce, don haka bai kamata a maye gurbin tattaunawa da tashin hankali ko amfani da barazana wajen hana mutane bayyana ra’ayoyinsu ba.
Tinubu ya gargadi 'yan siyasa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su tunkari duk wani nau’in daba da sauran ayyukan da suka saba wa zaman lafiya da tsarin dimokuradiyya da karfin doka.
Tinubu ya bayar da umarnin ne yayin da rahotannin tashin hankalin siyasa ke karuwa a sassan Najeriya gabanin babban zaben 2027.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban kasar ya yi Allah wadai da tashin hankali a lokacin yakin neman zabe, yana mai cewa ya kamata kamfen ya mayar da hankali kan manufofi da ra’ayoyin da za su inganta rayuwar al’umma.
Asali: Legit.ng

