2019: Ku zabi ‘Yan takarar da su ka cancanta inji Muhammadu Buhari

2019: Ku zabi ‘Yan takarar da su ka cancanta inji Muhammadu Buhari

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Shugaba Muhammadu Buhari, yayi kira ga mutanen Najeriya su zabi ‘Yan takarar da su ke da kima kuma su ka cancanta a zaben da za ayi a farkon 2019.

2019: Ku zabi ‘Yan takarar da su ka cancanta inji Muhammadu Buhari
Buhari yace jama'a su zabi 'Yan takara na gari a shekara mai zuwa
Asali: Twitter

Shugaban kasar na Najeriya ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da wasu Jagororin ‘Darikar Qadiriyya a Jihar Kano. Shugaban Hukumar nan ta TETFUND na kasa, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, shi ne ya wakilci Shugaban kasar a taron.

Shugaban kasar ya nuna yadda wadanda aka zaba kan mulki su ke da alhakin kare rayukan jama’a da kuma rike amanar baitul malin al’uma tare da hana handamar dukiyar Gwamnati, don haka ya nemi Jama’a su zabi mutane na gari a 2019.

KU KARANTA: Obasanjo ya fadi wasu da mutane da Allah ba zai bari su mulki Najeriya ba

Buhari, ta bakin Sakataren na Hukumar TETFund yake cewa burin sa shi ne ya dawo da Najeriya mutuncin da aka san ta da ita a baya, ko da dai taron addini ne aka yi ba na siyasa ba, Shugaban kasar ya fadakar da jama’a game da zaben badi.

Muhammadu Buhari ya yabawa Sheikh Nasiru Kabara wanda shi ne Jagoran Qadiriyya, a cewar sa, babban Malamin ya sadaukar da rayuwar sa wajen karantar da al’umma da kuma kokarin kawo zaman lafiya da fahimtar juna a fadin Duniya.

Shi ma dai Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara ya jinjinawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yace nutum ne mai fahimta da karbar shawara kuma wanda yake kokarin kawo gyara a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel