Alhaji Mohammed Lawal ya ga gana da Shugaba Buhari a fadar sa

Alhaji Mohammed Lawal ya ga gana da Shugaba Buhari a fadar sa

Labari ya zo mana cewa daya daga cikin Surukan Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarce sa a fadar Shugaban kasa na Aso Villa da ke cikin babban Birnin Tarayya Abuja a jiya Ranar Asabar da yamma.

Alhaji Mohammed Lawal ya ga gana da Shugaba Buhari a fadar sa
Mahaifin Mijin ‘Diyar Shugaba Buhari ya gana da Buhari a Fadar sa
Asali: Twitter

Kamar yadda mu ka ji, Alhaji Mohammed Lawal Sheriff ya sa labule da Mai Girma Shugaban kasa. Mai magana da bakin Shugaba Buhari watau Garba Shehu ne ya bayyana mana wannan ta shafin sa na sadarwa na Tuwita.

Hadimin Shugaban kasar bai dai bayyana abin da aka tattauna tsakanin Shugaban kasar da Surukin na sa ba. Mohammed Lawal shi ne Mahaifin Mohammed Babagana Sheriff wanda yake auren Halima Muhammadu Buhari.

KU KARANTA:

Alhaji Mohammed Lawal dai ‘Dan uwan ne wurin tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff. A 2012 ne Buhari ya aurawa Mohammed Lawal ‘Diyar sa Halima inda Marigayi Sarkin Borgu Halliru Danotoro ya tsaya mata.

Mun kuma samu labari daga fadar Shugaban kasar cewa Shugaba Buhari ya taya tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ken Nnamani murnar cika shekaru 70 da haihuwa a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: