Kasar Iran Ta Kai Mummunan Hari kan Amurka, Ta Sha Alwashin Nakasa Ta
- Dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai hari kan na’urar radar ta sojojin Amurka da ke sansanin Al-Riffa a Bahrain
- Hukumomin Bahrain sun ce sun dakile hare-haren jiragen sama marasa matuƙa na Iran, yayin da aka umarci mazauna yankin neman mafaka
- Iran ta yi barazanar ƙara tsananta hare-hare kan Amurka, tana mai cewa mashigar ruwan Hormuz na nan a rufe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Rahotanni sun bayyana cewa an ji ƙarar fashe-fashe a Bahrain bayan kasar Iran ta sake kai hari kan wani sansanin sojojin Amurka da ke ƙasar, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin.
Hare-haren sun faru ne da sanyin safiyar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, 2026, yayin da dakarun kare sararin samaniyar Bahrain suka shiga aikin dakile makaman da aka harba daga Iran.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun afkawa masallata a sallar asuba a Zamfara, an rasa rai yayin harin

Source: Facebook
Wannan hari ya zo ne kwanaki uku bayan da Bahrain ta sake fuskantar makamancin harin, bayan wani lokaci da aka samu raguwar hare-haren da ake kai wa ƙasar, cewar Al Jazeera.
An ji fashe-fashe sau biyu
Wani ɗan jarida ya bayyana cewa an fara jin fashe-fashe da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Lahadi, sannan mazauna yankin suka sake jin wasu fashe-fashe da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da gaggauta zuwa wuraren da ke da tsaro.
Haka kuma, ta shawarce su da su riƙa bibiyar bayanai daga hukumomin gwamnati domin kauce wa yaɗa jita-jita.
Rundunar sojin Bahrain ta ce ta yi nasarar tare wasu hare-haren Iran, inda ta bayyana cewa ta hana makaman isa wuraren da aka nufa.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta kuma tabbatar da cewa na'urorin kariya daga hare-haren sama sun kakkabo wasu jiragen yaƙi marasa matuƙa na Iran.

Source: Getty Images
Iran ta yi ikirarin kai hari kan sojojin Amurka
A nata ɓangaren, rundunar dakarun juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan wani tsarin radar na sojojin Amurka da ke sansanin jirage masu saukar ungulu na Al-Riffa a Bahrain.
A cewar sanarwar da gidan talabijin na ƙasar ya wallafa, an yi amfani da jirage marasa matuƙa guda shida wajen kai harin kan na'urar radar.
Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani mai tsanani kan duk wani sabon hari da Amurka za ta kai mata, cewar rahoton Punch.
Ta ƙara da cewa mashigar ruwan Hormuz na nan a rufe, tana mai cewa duk wani farmaki daga kasar Amurka zai fuskanci martani mafi ƙarfi.
Bahrain ta zargi Iran da kawo mata hari
Bahrain na daga cikin ƙasashen yankin Gulf da suka fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa tun bayan ɓarkewar yaƙin Gabas ta Tsakiya a ranar 28 ga Fabrairu.
Ma'aikatar harkokin wajen Bahrain ta bayyana cewa ƙasar ba za ta amince a mayar da yankinta wurin da ake amfani da shi wajen rama wa juna laifuffuka ba.
Ta kuma ɗora wa Iran alhakin hare-haren da sakamakonsu, tana mai cewa za ta ci gaba da kare martabar ƙasarta.
Trump zai dauki mataki kan Iran
An ji cewa Gwamnatin Amurka ta kafa sabuwar rundunar soji mai suna Task Force Iron Gate domin dakile safarar makamai.
Rundunar za ta mayar da hankali kan hana Iran samun fasahohin da ake amfani da su wajen kera makamai.
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta shigo da makamai, bama-bamai da manyan motoci da darajarsu ta kai dala biliyan biyu.
Asali: Legit.ng

