Zaben 2027: Atiku Ya Samu Tagomashi yayin da Tinubu Ya Gamu da Koma Baya a Arewa
- Ƙungiyar Tinubu Northern Youth Forum ta sanar da sauya matsayinta, inda ta janye goyon baya ga Tinubu tare da mara wa Atiku Abubakar baya
- Ƙungiyar ta sauya suna zuwa Arewa Youth For Atiku (AYA), domin faɗaɗa harkokin wayar da kan matasa da shiga siyasa a Arewacin Najeriya
- A ranar 14 ga Nuwamba, 2026, ƙungiyar za ta bayyana goyon bayanta ga Atiku tare da sanar da komawarta jam’iyyar ADC a Azare, jihar Bauchi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Wata ƙungiyar matasan Arewa mai suna Tinubu Northern Youth Forum ta sanar da janye goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da mara wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar baya.
Haka kuma, ƙungiyar ta sanar da sauya sunanta zuwa Arewa Youth For Atiku (AYA), a matsayin wani ɓangare na sabon matsayinta na siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
An bayyana wannan mataki ne cikin wata sanarwa da Adamu Jikan Manu ya sanya wa hannu a madadin ƙungiyar ranar Juma'a, 13 ga Nuwamba, 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Lokacin da za a bayyana goyon baya ga Atiku
Sanarwar ta bayyana cewa ƙungiyar za ta gudanar da bikin sanar da goyon bayanta ga Atiku, bayyana matsayinta na siyasa da kuma komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance.
Za a gudanar da taron ne a ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026, a ofishin dabarun siyasa na ADC da ke yankin Arewa maso Gabas, a garin Azare, jihar Bauchi.
Mai tattara ayyukan ƙungiyar, Hon. Auwal Ibrahim Sansani, CNA, ne zai jagoranci bikin sanarwar.
Dalilin sauya sunan ƙungiyar
A cewar sanarwar, sauya sunan Tinubu Northern Youth Forum zuwa Arewa Youth For Atiku na da manufar samar da babbar kafa da za ta haɗa matasa wajen tattaunawa da harkokin siyasa.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027
Ƙungiyar ta ce sabon tsarin zai kuma taimaka wajen wayar da kan jama’a, gudanar da ayyukan tallafa wa al’umma da kuma ƙarfafa shigar ’yan ƙasa cikin harkokin dimokuraɗiyya a faɗin Arewacin Najeriya.
Ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta, shugabannin al’umma da na addini, ƙungiyoyin matasa da mata, ɗalibai, ƙungiyoyin ’yan kasuwa da ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki da su halarci taron.
Saƙon ƙungiyar ga ’yan Najeriya
Sanarwar ta ce ƙungiyar na ganin Najeriya na buƙatar shugabanci nagari, haɗin kan ƙasa, ingantaccen tsarin mulki da kuma bai wa ’yan ƙasa damar taka rawa a harkokin tafiyar da ƙasar.
Ta kuma buƙaci ’yan Najeriya masu ra’ayin irin wannan manufa da su shiga cikinta domin gudanar da yakin neman zaɓe cikin lumana da bin tsarin dimokuraɗiyya gabanin babban zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta kammala sanarwarta da taken kamfen ɗinta mai cewa: “Ku shiga jirgin Atiku. Ku zaɓi Atiku, ku ceci Najeriya.”

Source: Twitter
An kori limami saboda Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi wasu ’yan siyasa, musamma gwamnoni, da tsangwamar mutanen da ke tare da shi.
Atiku Abubakar ya yi zargin cewa an dakatar da wani limami daga aikinsa na limanci bayan ya jagoranci sallar jam’in da ya halarta.
Asali: Legit.ng
