Jam'iyyar APC ta kawo wahala, ya kamata jama’a su zabi PDP - Zaka Sunday

Jam'iyyar APC ta kawo wahala, ya kamata jama’a su zabi PDP - Zaka Sunday

Wani jagoran matasa a jam’iyyar PDP, Kwamared Zaka D. Sunday ya zargi gwamnatin tarayya ta APC da jefa jama’a cikin wahala a Najeriya. Jaridar Daily Trust ce ta rahoto wannan labari a karshen makon nan.

Jam'iyyar APC ta kawo wahala, ya kamata jama’a su zabi PDP - Zaka Sunday

Gwamnatin APC tayi sanadiyyar wahalar da mutanen kasar nan
Source: Depositphotos

Comrade Zaka D. Sunday ya koka da cewa mutanen kasar nan sun shiga cikin halin ha’ula’i a dalilin gwamnatin Najeriya mai-ci. Sunday ya bayyana wannan ne a wajen wani taro da Matasan PDP su ka shirya a Garin Abuja.

Babban jagoran Matasan na PDP yake cewa gwamnatin Buhari ta gaza yin wani abin kirki musamman a fannin tattalin arziki. Wannan ya sa yayi kira ga mutanen Abuja su tabbata sun zabi jam’iyyar PDP a zaben 2019.

KU KARANTA: Abin da ya sa na bar Kwankwasiyya - ‘Dan takarar Majalisar UPC

Sanatan Yankin Abuja, Philip Aduda ya jinjinawa Matashin inda yace irin taron da aka shirya ya nuna cewa PDP za ta lashe zaben badi. Sanatan yayi kira ga ‘Ya ‘yan jam’iyyar su kara hada-kai domin a samu nasara a badi.

Yanzu haka jam'iyyar hamayya ta PDP tana zargin jama'a da jefa jama'a cikin hali na yunwa da matsanancin tsadar kayan abinci. Alkaluman kasa sun tabbatar da cewa ana fama da mugun rashin aikin yi a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel