Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari

Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari

Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyayen matukin jirgin Sojin Saman Najeriya, Baba-Ari da ya rasu sakamakon hatsarin jirgin da ya yi a ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba a Katampe, Abuja.

Jirgin Baba-Ari ya yi karo ne da wani jirgin na Sojin Saman Najeriya a yayin da suke shirye-shiryen bukukuwar zagoyowar samun 'yancin Najeriya a babban birnin tarayya Abuja.

Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa

Shugaban hafsoshin Sojin Saman Najeriya, AVM Abubakar Saddiq tare da wasu jiga-jigan Sojojin Najeriya da masu fada a ji duk sun hallarci jana'izar marigayi Baba-Ari wanda ya rasu sa'o'i kadan bayan afkuwar hatsarin.

Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Asali: Twitter

Sauran matukan jirgin da hatsarin ya ritsa dasu suna asibiti inda suke samun kulawar likitoci.

Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Asali: Twitter

Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya gidansu Baba-Ari
Asali: Twitter

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wani dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Labour Party na jihar Kwara, Issa Arewa ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari ya karrama marigayi Baba-Ari da lambar yabo na kasa saboda ya sadaukar da rayuwansa ne wajen yiwa kasarsa hidima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel