Ana Shirin Zaben 2027, NDLEA Ta Gano Masana'antar Kera Bindigogi a Kaduna
- Jami’an NDLEA sun gano wata masana’antar kera bindigogi a yankin Sabon Garin Kangin da ke jihar Kaduna
- Hukumar ta ce ta ƙwato bindigogin da aka riga aka ƙera da kuma kayan aikin da ake amfani da su wajen kera wasu makamai
- NDLEA ta kama wanda ake zargin mamallakin masana’antar, inda ta danganta gano wurin da alaƙar safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuffuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta gano wata masana’antar kera bindigogi a jihar Kaduna, inda ta ƙwato makamai da kayayyakin da ake amfani da su wajen ƙera bindigogi.
Hukumar ta kuma kama wanda ake zargin mamallakin masana’antar yayin samamen da jami’anta suka kai yankin Sabon Garin Kangin da ke jihar.

Source: Facebook
Daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a cikin wani rahoton yanayin safarar miyagun ƙwayoyi da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2026.
Abin da jami’an NDLEA suka gano
A cewar Babafemi, jami’an hukumar sun kai samame yankin ne kwanakin baya, inda suka gano wurin da ake ƙera bindigogi.
Ya ce a yayin samamen, jami’an sun ƙwato bindigogin da aka riga aka kammala ƙerawa, tare da wasu kayayyaki da aka tanada domin ƙera ƙarin makamai.
A cikin sanarwar, Babafemi ya ce:
“Yayin wani samame da jami’an NDLEA suka kai yankin Sabon Garin Kangin da ke Kaduna kwanakin baya, sun gano masana’antar kera bindigogi. Sun ƙwato bindigogin da aka riga aka ƙera da kayan aikin samar da wasu makamai, tare da kama mamallakin wurin.”
Sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin bindigogin da aka ƙwato ko kuma cikakken bayanin mutumin da aka kama ba.
Alaƙar miyagun ƙwayoyi da laifuffuka
Babafemi ya bayyana cewa gano masana’antar ya ƙara nuna alaƙar da ke tsakanin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, safarar su da sauran ayyukan ta’addanci da laifuka.

Kara karanta wannan
APC ta yi gyara a kwamitin kamfen din Tinubu bayan an yi abun kunya a idon duniya
Ya ce wannan lamari ya sake tabbatar da cewa matsalar shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi na iya kasancewa da alaƙa da wasu nau’ukan aikata laifuka.
A kalamansa, ya ce:
“Wannan ya ƙara tabbatar da abin da aka riga aka sani, cewa akwai alaƙa tsakanin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, safarar su da sauran nau’ukan aikata laifuka.”
Hukumar ba ta ƙara bayyana matakan da za ta ɗauka kan wanda aka kama ko kuma yadda binciken lamarin ke gudana ba.

Source: Original
NDLEA ta cafke mata dauke da bindigu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun kama wata mata mai suna Aisha Isah da alburusai 266 na bindigar AK-47 a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
An kama matar ne a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan hanyar yayin da jami’an hukumar ke gudanar da sintiri a kan hanyar.
Asali: Legit.ng
