Aisha Buhari ta nemi hadin kan Musulmi da Kirista wajen yakar keta haddin Mata a Jami'o'in Najeriya
Uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta yi kira kan hadin kan manyan addinai biyu na kasar nan domin tunkarar annobar cin zarafi da keta haddin Mata a jami'o'i, wuraren aiki da kuma tsakanin iyalai a kasar nan ta Najeriya.
Hajiya Aisha ta yi wannan kira ne yayin gabatar da wata lacca mai taken Rayuwar Musulmai cikin zamantakewar al'umma a da gidauniyarta ta Aisha Buhari Foundation ta dauki nauyin shiryawa a jiya Asabar cikin dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa a babban birnin kasar nan na tarayya.
Uwargidan ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa, babbar manufar wannan lacca itace aika sako zuwa ga Matasa da za su fuskanta tare da wa'azantuwa kan tafarkin addinin su na Musulunci domin kubuta daga turba ta halaka a rayuwar su ta yau da kullum.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Hajiya Aisha ta nemi hadin kai tsakanin kungiyar Jama'atu Nasril Islam da kuma cibiyar kolu kan harkokin Addinin Musulunci wajen gindaya tsare-tsare da kyawawan akidu ga Musulman Najeriya.

Asali: Depositphotos
Ta ci gaba da cewa, baya ga karatun Al-Qur'ani akwai kuma muhimmiyar bukata ta bibiyar tafarkin hanyoyin shiriya da Ayoyin sa suka kunsa tare da sanya su cikin al'amurran mu na yau da kullum domin gujewa halaka da tabbatuwa kan tafarkin tsira.
KARANTA KUMA: Mu sanya dorewar ci gaban Najeriya cikin addu'o'in mu - Osinbajo
A sanadiyar Uwargidan shugaban kasar ta yi kira kan dukkanin manyan addinai biyu da su hada gwiwa da juna wajen tsarkake kasar nan daga annobar cin zarafi da keta haddin Mata musamman a jami'o'i, wuraren aiki da sauraran wuraren da ake cudanya Maza da Mata.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a jiya Juma'a Uwargidan shugaban kasa ta bayyana takaicinta dangane da Mutuwar wata Budurwa mai shekaru 13 a duniya, Elizabeth Ochanya Ogbanje, da ta yi gamo da ajali a sakamakon cin zarafi da keta haddi da ta fuskanta a jihar Benuwe.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng