Abin da na Jikin Tinubu Suka Gano Wanda Ya Nuna Arewa na Tare da Shugaban Ƙasa
- Mohammed Idris ya ce taron APC da aka gudanar a Jos ya nuna yadda magoya bayan jam'iyyar ke kallon gwamnatin Tinubu
- Ministan ya ce manufofin tattalin arziki da ayyukan raya ƙasa na daga cikin abubuwan da ke ƙara wa gwamnatin farin jini
- Ya buƙaci 'yan adawa su gabatar da tsare-tsaren da za su amfanar da Najeriya maimakon mayar da hankali kan sukar gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, ya bayyana yadda Bola Tinubu ke samun karbuwa.
Idris ya ce halartar dubban magoya bayan APC a taron siyasar da aka gudanar a Jos, babban birnin jihar Filato, na nuni da yadda jam'iyyar ke samun goyon baya a yankin Arewa ta Tsakiya.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC da aka gudanar ranar Asabar wanda ma'aikatar yada labarai ta wallafa a shafin Facebook.
Yadda masoyan Tinubu suka amince da shi
Idris ya nuna yadda magoya bayan jam'iyyar ke kallon manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da matakan da gwamnatinsa ke ɗauka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
A cewar ministan, yawan mutanen da suka fito domin halartar taron na iya zama alamar yadda wasu daga cikin 'yan Najeriya ke kallon ayyukan gwamnatin tarayya da ƙoƙarinta na magance matsalolin ƙasar.
Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen samar da yanayin da zai ba tattalin arzikin Najeriya damar bunƙasa, tare da ƙara yawan ayyukan raya ƙasa da samar da damarmakin dogaro da kai.
Ya ce gwamnati na son ganin sauye-sauyen da take aiwatarwa sun wuce matakin manufofi kawai, su zama abubuwan da jama'a za su iya gani kuma su amfana da su a rayuwarsu ta yau da kullum.
Ministan ya ƙara da cewa Bola Tinubu ba ya shirin yin watsi da tsare-tsaren da ya fara aiwatarwa, inda ya jaddada cewa ci gaba da aiwatar da su na daga cikin matakan gina tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su duba irin sauye-sauyen da ake ƙoƙarin samarwa, yana mai cewa manufar gwamnati ita ce gina ƙasa mai tattalin arziki mai ƙarfi da kuma kyakkyawar makoma.

Source: Twitter
Idris ya soki salon siyasar 'yan adawa
Ministan ya kuma yi kira ga jam'iyyun adawa da su sauya yadda suke gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe, inda ya buƙace su da su fito da manufofi da za su nuna irin sauyin da suke son kawo wa ƙasar.
Ya ce siyasar dimokiraɗiyya bai kamata ta kasance ta hanyar kushe gwamnati da yin maganganu kawai ba, yana mai cewa ya kamata 'yan siyasa su gabatar da shawarwarin da za su iya inganta rayuwar al'umma.
A cewarsa, Najeriya na buƙatar siyasar da za ta bai wa jama'a damar tantance manufofin 'yan takara, tare da samun zaɓuɓɓukan shugabanci masu inganci.
Idris ya kuma yi nuni da cewa shirye-shiryen babban zaɓen 2027 na buƙatar dukkan jam'iyyun siyasa su taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da mutunta tsarin dimokiraɗiyya.
Matasa sun bar Tinubu saboda Atiku
A wani labarin, an ji cewa wata kungiyar matasa a Arewa mai suna Tinubu Northern Youth Forum ta janye goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu, inda ta koma bayan Atiku Abubakar.
Kungiyar ta sauya sunanta zuwa Arewa Youth For Atiku (AYA), domin fadada harkokin wayar da kan jama'a da shiga harkokin siyasa a yankin Arewa.
Ta sanar da shirin sauya sheka zuwa ADC tare da bayyana goyon bayanta ga Atiku a wani taro da aka shirya gudanarwa a Azare, jihar Bauchi.
Asali: Legit.ng


