Aisha Buhari da Dolapo Osinbajo sun samu sabbin makamai a gwamnatin tarayya
A jiya, Litinin, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wasu kwamitoci da zasu samar da hanyoyin da za a magance matsalar karuwar tu'ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da ma ragowar 'yan Najeriya.
Yayin kafa kwamitocin, shugaba Buhari ya nada uwargidansa, Aisha Buhari, da ta mataimakinsa, Dolapo Osinbajo, a matsayin mambobi a cikin kwamitocin.
Shugaban kasa ya nada tsohon gwamnan jihar Legas, Janar Buba Marwa (mai ritaya), a matsayin shugaban kwamitin da Aisha da Dolapo ke matsayin mambobi.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Da duminsa: Dan majalisar tarayya daga Katsina ya fice daga APC ya koma PDP
Da yake gabatar da jawabi yayin rantsar da kwamitocin, shugaba Buhari ya ce ya saka uwargidansa da ta mataimakinsa ne domin su taimaka wajen fitowar mata domin a dama da su a yaki da shan miyagun kwayoyi.
Daga cikin ragowar mambobin kwamitin da Marwa zai jagoranta akwai wakilan matan gwamnonin Najeriya, wakilan hukumar kwastam, NAFDAC, NDLEA, 'yan sanda, da sauransu.
Buhari ya koka a kan karuwar da matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi ke kara yi a kasar nan, musamman batun rahoton hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi NDLEA) da ya bayyana cewar ana shan miliyoyin kwalaben kodin kowacce a rana a iya jihar Kano kawai.
Kazalika ya yi kira ga dukkan jama'a da su bayar da gudunmawa ta hanyoyin da suka dace domin yakar wannan annoba dake barazanar lalata al'ummar Najeriya bakidaya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng