Aisha Buhari ta hori al'ummar Kasa akan gujewa munanan kalamai game da Najeriya
Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, Uwargidan Shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari, ta hori al'ummar kasar nan tare da gargadin su kan kauracewa aibata Najeriya da munanan kalamai da cewar akwai tasirin cikin kowane nau'i na furuci.
Aisha Buhari ya bayar da wannan muhimmiyar shawara ga al'ummar kasar nan yayin halartar wani babban taro a Cocin Cathedral of Holy Trinity dake unguwar Gwagwalada a babban birni na tarayya.
Misis Grace Chamah, uwargidan tsohon gwamnan jihohin Katsina da Kebbi a lokacin mulkin soja, ita ta wakilci uwargidan ta shugaban kasa da aka karrama yayin wannan taro kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Asali: Depositphotos
Cikin wata sanarwa da kakakin uwargidan shugaban kasa ya bayyana, Suleiman Haruna, ya bayyana cewa akwai tasirin gaske cikin kowane nau'in furuci da uwargijiyarsa ke shawartar al'ummar kasar nan akan furta kyawawan kalamai ga kasar su.
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nemi Sarakunan Gargajiya su zamto Limaman hadin kai ga al'ummomin su
Hajiya Aisha ta kuma nemi a ci gaba da kwarara addu'o'i ga shugabanni domin hakan zai taimaka kwarai da aniyya wajen karkatar akalarsu ta inganta rayuwa da kuma dadawa al'ummar kasar nan.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaba Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun yi Allah wadai kan aukuwar wani sabon rikici da ya salwantar da rayukan Mutane 55 a Kasuwar Magani dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng