Lamari Ya Yi Tsanani har kotu Tana Yi wa Ministan Tinubu Barazana da Dauri a Kurkuku
- A shekarar 2024 aka cafke wasu shugabannin al’umma a yankin Neja Delta sakamakon kashe sojoji da aka yi
- Kotu ta yi wa Babban lauyan Gwamnatin Najeriya kuma Ministan Shari'a kashedi a fito da wadannan mutane
- Idan Lateef Fagbemi ya ki bin wannan umarni, alkalin kotun tarayya ya yi maza barazanar kai shi gidan gyaran hali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Delta - Babbar Kotun Tarayya da ke Warri a jihar Delta ta yi barazanar daure Babban lauyan Gwamnatin Najeriya kuma Ministan Shari'a.
Lateef Fagbemi ya fusata alkali saboda zargin kin bin umarnin kotu na sakin wasu shugabannin al'ummar Okuama da ake tsare da su har yanzu.

Source: Getty Images
Kotu ta yi wa Ministan shari'a kashedi
Gargadin na kunshe ne a cikin takardar wani fam, mai taken Sanarwa kan Sakamakon Saba umarnin Kotu kamar yadda The Cable ta fada.
Takardar ta gargadi Lateef Fagbemi SAN cewa idan ya gaza bin umarnin kotu na sakin wadanda ake tsare da su, hakan zai zama ya raina kotu.
An fitar da wannan fam ranar 11 ga Nuwamba, 2026 inda aka fada wa ministan za a iya daure shi.
Kotu ta ce:
“A kiyaye cewa idan ba a bi umarnin da kotu ta yin a gaggauta sakin masu kara na 1, 2, 4, 5 da 6 daga inda suke tsare ba, za a same ka da laifin raina kotu kuma zai jawo a iya daure ka a gidan gyaran hali.
Jami'an tsaro sun kama shugabannin Neja Delta
Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da Hyeladzira Nganjiwa ya yanke a ranar 10 ga Yuni, 2026, lokacin ya yi umarni a saki wadannan Bayin Allah.
Ya bayar da umarnin sakin shugabannin al'ummar Okuama da jami’an tsaro suke tsare da su.
Wadanda aka ambata a karar sun hada da Arthur Ekpekpo, James Oghoroko, Bernard Esegba, Belvis Adogbo, Dennis Okugbaye da Mabel Owhemu.
Sahara Reporters ta ce sun ce sojoji sun kama shugabannin tun watan Agustan 2024, bayan kashe sojojin Najeriya 17 a ranar 14 ga Maris, 2024 a Delta.
Mutane 2 sun mutu a hannun Sojojin Najeriya
Daga cikin wadanda aka tsare akwai James Oghoroko, tsohon shugaban al'ummar Okuama, da Dennis Okugbaye, ma'ajin al'ummar mai shekaru 81.
Rahotanni sun ce dukkansu biyu sun mutu ne a hannun sojojin Najeriya yayin da suke tsare.
Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta taba bayyana cewa tana gudanar da bincike kan rahotannin mutuwar amma dai zuwa yanzu ba a ji wani labari ba.

Source: Getty Images
Sojojin da aka kashe wa Najeriya a Neja Delta
An ji cewa Hedkwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta wallafa sunaye da hotunan jami'an rundunar sojojin 17 da aka kashe a ƙauyen Okuama a jihar Delta.
Waɗanda suka rasa rayukansu sun haɗa da laftanar kanal, manjoji, kyaftin, da sauran dakarun soji yayin da suke gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya.
Lamarin ya jawo maganganu daga 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta, inda da dama ke miƙa ta'aziyya yayin da wasu ke neman a hukunta masu laifi.
Asali: Legit.ng

