Dangote Ya Dauki Nauyin Bikin Baje Kolin Noma na 2026, Abinci Zai Wadata a Arewa
- Rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana sabon shirin bunƙasa harkar noma a Arewacin Najeriya domin ƙara samar da abinci da rage rashin aikin yi
- Kamfanin na shirin ƙarfafa noman zamani da masana'antun sarrafa amfanin gona, ciki har da shinkafa da sukari
- Gidauniyar Noma ta Ƙasa ta buƙaci Aliko Dangote ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen kawo sauyi a harkar noma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Kamfanin Dangote Industries Limited (DIL) ya bayyana aniyarsa ta ƙara zuba kuɗaɗe a harkar noma a Arewacin Najeriya, a wani yunƙuri na ƙara wadatar abinci, bunƙasa tattalin arzikin karkara da samar da hanyoyin samun aikin yi.
Sabon shirin kamfanin ya ƙunshi bunƙasa gonakin zamani, faɗaɗa masana'antun sarrafa shinkafa a jihohin Arewa da kuma ƙarfafa ayyukan masana'antun sukari.

Source: Facebook
Shirin da Dangote ya yi kan noma
Shugaban sashen hulɗa da jama'a na rukunin kamfanonin, Anthony Chiejina, ne ya bayyana waɗannan tsare-tsare cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar NAN.
Sanarwar ta ƙunshi bayanan da daraktar shiyyar kamfanin, Fatima Wali-Abdurrahman, wadda kuma babbar mai ba Aliko Dangote shawara ce, ta gabatar dangane da shirin faɗaɗa harkokin noma.
A cewarta, kamfanin na ganin akwai gagarumar damar bunƙasa noma a Arewacin Najeriya, don haka yake ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan da za su taimaka wajen rage dogaro da abincin da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.
Ta kuma jaddada cewa samar da takin zamani a cikin gida na daga cikin manyan hanyoyin da kamfanin ke tallafa wa manoma.
Wannan zai ba su damar samun kayan aikin gona cikin sauƙi tare da inganta yawan amfanin gonakinsu.
Dangote ya shiga shirya babban bikin noma na ƙasa
A wani mataki na nuna goyon bayansa ga bunƙasa harkar noma, kamfanin Aliko Dangote zai ɗauki nauyin babban bikin baje kolin noma na Najeriya na shekarar 2026, wanda ake sa ran fara gudanarwa ranar Litinin.

Kara karanta wannan
2027: Gwamna ya ce nasarorin da ya samu za su taimaka masa wajen zama shugaban ƙasa
Gidauniyar Noma ta Ƙasa ta Najeriya (NAFN) ce za ta jagoranci taron, ƙarƙashin kulawar Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari.
Anthony Chiejina ya bayyana cewa manufar kamfanin ba ta tsaya ga tallafa wa samar da abinci kawai ba, domin yana son ganin mata da matasa sun samu cikakkiyar dama wajen shiga harkokin noma da kasuwancinsa.
Ya ce Najeriya na da albarkatun ƙasa da dama da za su iya mayar da ita babbar cibiyar samar da kayayyakin noma a nahiyar Afirka idan aka samar da isasshen jari da ingantattun tsare-tsare.

Source: UGC
Gidauniyar Noma ta buƙaci Dangote ya ƙara zuba jari
Ko'odinetar Ƙasa ta NAFN, Hajiya Aishatu Ibrahim, ta bayyana cewa taken bikin baje-kolin na shekarar 2026 shi ne: “Gina tsarin noma mai juriya a Najeriya: Ƙarfafa manoma, haɗa jari da haɓaka sababbin dabaru don tsaron abinci da raba arziki.”
Ta ce an tsara taron ne domin samar da mafita ga matsalolin da ke hana harkar noma bunƙasa, ta hanyar haɗa masu ruwa da tsaki da kuma samar da damar haɗin gwiwa tsakanin manoma da masu zuba jari.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027
A cewarta, taron zai ba masu tsara manufofi, ƙwararrun masana, masu samar da fasaha da 'yan kasuwa damar tattauna hanyoyin inganta harkar noma da tabbatar da samun wadataccen abinci a Najeriya.
Dangote ya magantu kan hannun jari
Mun ba ku labarin cewa tayin hannun jarin matatar mansa bai cimma burin jawo masu zuba jari miliyan 10 ba.
Sai dai ya ce tayin ya samu gagarumar karɓuwa daga miliyoyin mutane duk da ƙarancin lokacin da aka ba da dama.
Rahoto ya nuna cewa an samu wadanda suka nemi sayen hannun jari ta Naira tiriliyan 6.4, kusan ninki uku na adadin da aka yi niyyar sayarwa.
Asali: Legit.ng
