Dalilan da ake Gani za Su Iya Sa Atiku Ya Yi Nasara a kan Tinubu a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na kara kokarin neman goyon bayan al’ummar Arewa gabanin zaben shugaban kasa na 2027
- Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa wasu magoya bayan marigayi Muhammadu Buhari na karkata zuwa Atiku
- Rashin gamsuwar wasu ’yan Najeriya kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da matsalolin tattalin arziki na daga cikin abubuwan da ka iya shafar zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na kara jan hankalin jama’a kan kudirinsa na sake neman kujerar shugaban kasa a zaben 2027.
Atiku na da dimbin alaka da magoya baya a Arewa, lamarin da ka iya taimaka masa wajen kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke da damar da ke tattare da kasancewa a kan karagar mulki da kuma tsarin siyasar APC.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa kokarin Atiku na sake gina karfinsa na siyasa, yiwuwar sauyin matsayar wasu magoya bayan marigayi Muhammadu Buhari da kuma korafe-korafen tattalin arziki na cikin abubuwan da ake ganin za su iya tasiri a zaben mai zuwa.
Atiku ya karfafa alaka da Arewa
Atiku ya mayar da hankali wajen karfafa goyon bayan masu kada kuri’a a Arewa, inda ya bukaci magoya bayansa a Sakoto su hada kai da iyalansu, abokansu da sauran al’umma domin fitowa rumfunan zabe.
A lokacin kamfen, Punch ta rahoto cewa ya kuma bukace su da su tabbatar sun kare kuri’unsu, tare da ganin an kirga su kuma an bayyana sakamakonsu.
Atiku ya yi gargadin cewa rashin fitowar magoya bayan jam’iyyun adawa da yawa na iya rage tasirinsu a zabe.
Ya ce:
“Ina rokon kowannenku da ya fito, ya hada iyalansa, abokansa da duk masu yi masa fatan alheri. Ku kada kuri’a sosai, ku kare kuri’unku, kuma ku tabbatar an kirga kuri’unku tare da bayyana sakamakonsu.”

Kara karanta wannan
Dan majalisar Kano ya faɗi lokacin da mulki zai dawo Arewa, ya roƙa wa Tinubu alfarma
Alakar mutanen Buhar da Atiku
Wani sabon batu da ya kara jan hankali a siyasar Arewa shi ne ikirarin tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, cewa wasu magoya bayan marigayi Muhammadu Buhari na karkata zuwa Atiku.
Dalung, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC kuma ya yi aiki a gwamnatin Buhari, ya danganta hakan da ziyarar da matar marigayin, Aisha Buhari, ta kai wa Atiku.
Ya bayyana cewa ziyarar na nuna yiwuwar sauyin matsayar wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar.
Dalung ya ce:
“Sakon da ta kai shi ne, duk wani dan siyasa ya sani cewa an yi nasarar mika kuri’u miliyan 12. Mun samu kira ta waya daga kabarin Buhari cewa mu zabi Atiku.”
Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa Atiku zai iya kayar da Tinubu a zaben 2027, duk da kalubalen da jam’iyyar da yake cikinta ke fuskanta.
Matsin tattalin arziki da zaben 2027
Baya ga lissafin siyasar Arewa, halin tattalin arzikin Najeriya na daga cikin batutuwan da ka iya yin tasiri a zaben shugaban kasa na 2027.
Tsadar rayuwa, hauhawar farashin abinci, rashin aikin yi da matsalar tsaro sun kara jawo korafe-korafe daga wasu al’ummar kasar kan yadda ake tafiyar da gwamnati.

Source: Facebook
A bangaren Atiku, damar da yake da ita ita ce mayar da wadannan korafe-korafe zuwa kuri’u ta hanyar gabatar da ingantattun tsare-tsare kan tattalin arziki, tsaro da samar da ayyukan yi.
Tinubu ya roki 'yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci al’ummar jihar Edo su sake zabensa a wa’adi na biyu domin ya kammala ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta fara.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu a gangamin yakin neman zaben APC a birnin Benin, ne ya bayyana bukatar shugaban kasar.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka a fannonin tituna, wutar lantarki da kiwon lafiya a jihar, yana mai rokon al’ummar Edo su ba shi damar kammala su.
Asali: Legit.ng

