Aisha Buhari ta taya mata 2 da suka samu nasara a zaben fitar da gwani na takarar Sanata murna

Aisha Buhari ta taya mata 2 da suka samu nasara a zaben fitar da gwani na takarar Sanata murna

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta taya wasu mata biyu da suka samu nasara a zaben idda gwani na takarar kujerun sanata guda biyu na jam’iyyar APC a jahar Adamawa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Matan da suka samu wannan gagarumar nasara sun hada da Sanata Binta Masi Garba, wakiliyar al’ummar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya, da kuma Aishatu Dahiru dake neman darewa kujerar Sanatan jama’a Adamawa ta tsakiya.

KU KARANTA: Murnar zabe: Wani Matashi ya nufi Abuja a kasa daga garin Zaria saboda nasarar Atiku

Aisha Buhari ta taya mata 2 da suka samu nasara a zaben fitar da gwani na takarar Sanata
Binta da Binani
Asali: UGC

Aisha Buhari ta sanar da haka ne ta bakin mai magana da yawunta, Suleiman Haruna a ranar Talata 9 ga watan Oktoba, inda tace nasarar da matan suka samu zai baiwa sauran mata kwarin gwiwar shiga harkokin siyasa tare da tsayawa takara.

“Ina addu’ar ganin matan guda biyu da dukkanin sauran matan da suka samu nasarra lashe zaben fidda gwani suka samu tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC su samu nasara a babban zaben shekarar 2019.” Inji Aisha.

A yayin da take kira ga yan takarkarun da su tsaya tsayin dake wajen cika manufofin jam’iyyar APC, ta yi kira gay an takarkarun da su baiwa ayyukan cigaban mata fifiko, tare da samar da tsare tsare da zasu taimaka ma talakawa, idan suka samu nasara a babban zabe mai zuwa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a matsayinta na sabuwar yanka a siyasa, Aisha Binani ta samu nasarar zama yar takarar jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Adamawa ta tsakiya bayan ya kayar da tsohon shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya,Umar Umarana da wata yar takara mace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel