APC Ta Bayyana Tsarin Tinubu na Kawo Karshen Rashin Tsaro a Najeriya
- APC-PCC ta ce Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin sojoji 28,000 da jami’an ’yan sanda 50,000 domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro
- Kwamitin ya bayyana cewa an kafa sababbin rundunonin soji huɗu, tare da gina cibiyoyin horas da sababbin sojoji a Osun da Ebonyi
- APC-PCC ya yi ikirarin cewa an kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga sama da 15,000 cikin shekaru uku, yayin da mayakan Boko Haram sama da 130,000 suka miƙa wuya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin Kamfen din Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC (APC-PCC) ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na shirin samar da sabon tsarin dabarun yaƙi da matsalar tsaro na tsawon shekaru biyar.
Kwamitin ya kuma bayyana cewa Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin jami’an tsaro 78,000, domin ƙarfafa ayyukan sojoji da ’yan sanda wajen magance matsalar tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin

Source: Twitter
Mai magana da yawun kwamitin, Dele Alake, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2026 a shafin Facebook, inda ya yi bayanin matakan da gwamnatin ke shirin ɗauka.
Sabon tsarin tsaro na shekaru 5
A cewar sanarwar, shirin da aka kira Five-Year Strategic Defence Operations Plan zai samar da tsarin da zai haɗa ayyukan soji, horaswa, kayan aiki da kashe kuɗaɗe bisa la’akari da matsalolin tsaron Najeriya.
Kwamitin ya ce tsarin zai mayar da hankali kan haɗin gwiwar hukumomin tsaro, tattara bayanan sirri da amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuka.
Ya kuma bayyana cewa shirin zai taimaka wajen tsara yadda gwamnati za ta kashe kuɗaɗen tsaro bisa barazanar da ake fuskanta da kuma buƙatun gudanar da ayyukan soji.
APC ta yi ikirarin kashe ’yan ta’adda 15,000
Sanarwar ta kuma bayyana sakamakon ayyukan soji a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, inda ta yi ikirarin cewa an kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga sama da 15,000 cikin shekaru uku da suka gabata.
Kwamitin ya ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram da waɗanda suka dogara da su sama da 130,000 ne suka miƙa wuya ta hanyar shirin Operation Safe Corridor.
Shirin Operation Safe Corridor wani tsari ne na gwamnatin tarayya da aka ƙirƙira domin gyara da sake shigar da tsofaffin ’yan tada ƙayar baya cikin al’umma bayan sun tuba.
APC-PCC ya ce waɗannan alkaluma na nuna yadda gwamnatin Tinubu ke haɗa ayyukan soji da wasu hanyoyin da ba na amfani da ƙarfi ba wajen magance matsalar tsaro.
Gwamnati za ta ɗauki ƙarin jami’an tsaro 78,000
Sanarwar ta ce Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin sojoji 28,000 da kuma jami’an ’yan sanda 50,000 domin ƙara yawan jami’an da za su gudanar da ayyukan tsaro a faɗin ƙasar.
Haka kuma, kwamitin ya bayyana cewa an ƙirƙiri sabbin rundunonin soji huɗu, yayin da aka sake fasalta wasu tsoffin rundunoni domin faɗaɗa wuraren gudanar da ayyukansu da inganta martanin da suke bayarwa kan barazanar tsaro.
Sababbin cibiyoyin horas da sojoji a Osun da Ebonyi
Gwamnatin ta kuma amince da kafa ƙarin cibiyoyin horas da sojoji guda biyu a Osogbo, jihar Osun, da Amasiri-Edda, jihar Ebonyi.
A cewar kwamitin, kowace cibiyar za ta iya ɗaukar sababbin sojoji 6,000 a lokaci guda domin horas da su. Sanarwar ta ce tuni aka fara horas da sababbin sojoji 5,210 a cibiyar Osogbo.
APC-PCC ya bayyana cewa waɗannan cibiyoyi za su rage lokacin da ake ɗauka wajen horas da sababbin sojoji, tare da ƙara yawan waɗanda za a iya tura su bakin aiki.
Gwamnati za ta gina barikin sojoji a Ekiti
Majalisar ta kuma yi nuni da zuba jari a gine-ginen barikokin sojoji da sauran kayayyakin more rayuwa da ke taimaka wa ayyukan tsaro.
Daga cikin ayyukan akwai gina barikin sojoji mai gidaje 700 a Ikere-Ekiti, jihar Ekiti. Ta ce aikin zai inganta yanayin rayuwa da wuraren aiki na jami’an soji, tare da samar da muhimman abubuwan more rayuwa da za su tallafa wa ayyukansu.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana takamaiman lokacin da za a fara aiwatar da sabon tsarin tsaro na shekaru biyar ba.

Source: Facebook
Dino Melaye ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar ADC, Sanata Dino Melaye, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jefa ’yan Najeriya cikin matsananciyar yunwa da wahalhalun tattalin arziki.
Melaye ya bayyana cewa Tinubu bai cancanci sake samun wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa ba, inda ya bukaci ’yan Najeriya su kaɗa ƙuri’unsu domin sauya gwamnatin APC a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

