Zaben 2027: Kwankwaso Ya Fadi Halin Peter Obi da Ya Bambanta Shi da Saura

Zaben 2027: Kwankwaso Ya Fadi Halin Peter Obi da Ya Bambanta Shi da Saura

  • Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana Peter Obi a matsayin mutum mai gaskiya da ba ya da alaƙa da cin hanci
  • Kwankwaso ya ce gwamnatin NDC za ta ba da fifiko ga ilimi kyauta domin yara su samu damar zuwa makaranta ba tare da matsalar kuɗi ba
  • Peter Obi ya yi alƙawarin farfaɗo da masana’antun Kano da suka daina aiki domin bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Kwankwaso, ya bayyana ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar, Peter Obi, a matsayin mutum mai gaskiya da ba ya karɓar cin hanci.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2026 yayin bikin yaye ɗalibai karo na biyar na Jami’ar Skyline ta Najeriya da ke Kano.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Amaechi ya bar gwamnatin Atiku idan suka hau mulki

Kwankwaso ya yabawa Peter Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya ce wannan hali na Obi na da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da shugabanci nagari a Najeriya, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.

Kwankwaso ya yaba da halayen Peter Obi

Tsohon gwamnan Kano ya ce a cikin watannin da suka yi suna aiki tare, ya fahimci cewa Obi ba mutum ne da ake zargin yana da alaƙa da cin hanci da rashawa ba.

A kalamansa:

“Abu ɗaya da na lura da shi a cikin watannin baya-bayan nan da muka yi muna aiki tare shi ne, Peter Obi mutum ne mai gaskiya, wanda ba ya karɓar cin hanci.
“Ba mutum ne da za ka fara tunanin cewa akwai alaƙa tsakaninsa da cin hanci ba. Wannan hali yana da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da shugabanci a wannan ƙasa.”

Kwankwaso ya kuma yi alƙawarin cewa idan NDC ta kafa gwamnati, za ta ba da fifiko ga ilimi kyauta domin babu wani yaro da zai rasa damar zuwa makaranta saboda rashin kuɗin makaranta.

Kara karanta wannan

"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya

Ya ce shi da Obi suna da ra’ayoyi iri ɗaya a fannoni da dama, musamman batun inganta ilimi. Ya bayyana burinsu na ganin cewa babu wani yaro da zai shiga ƙunci har ya riƙa bara domin samun abin da zai ci.

Kwankwaso ya ƙara da cewa suna shirin samar da ilimi kyauta domin yaran da iyayensu ba za su iya biyan kuɗin makaranta da sauran buƙatun karatu ba su rasa damar samun ilimi.

Obi ya yi alƙawarin farfaɗo da masana’antun Kano

A nasa jawabin, Peter Obi ya yi alƙawarin farfaɗo da masana’antun Kano da suka daina aiki domin farfaɗo da harkokin tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

Ya bayyana Kano a matsayin muhimmiyar jiha wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa dole ne a fara ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar daga jihar.

“Idan muna son gyara Arewa da Najeriya, dole ne mu fara daga Kano. Wannan birni shi ne ruhin Najeriya.” In ji shi.

Ya kuma shawarci waɗanda suka kammala karatu da su rungumi sana’o’i da harkokin kasuwanci, yana mai cewa ƙananan sana’o’i da kasuwanci na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

"Karya suke yi": Tinubu ya sake magana kan dawo da tallafin man fetur

Kwankwaso ya yi magana kan Peter Obi
Peter Obi tare da Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Peter Obi ya daukarwa 'yan Najeriya alkawari

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin magance matsalar ’yan Najeriya da rikice-rikicen tsaro suka tilasta barin gidajensu.

Peter Obi ya bayyana cewa gwamnatinsa ta zama wadda ta gaza idan har wani ɗan Najeriya yana zaune a sansanin ’yan gudun hijira (IDP) bayan watanni 18 da kama aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng