Shugaban Kasa Tinubu Ya Amince a Dauki Sababbin Sojoji 28000 da ‘Yan Sanda 50000 Aiki
- Shirin tsaro na shekaru biyar da Gwamnatin Bola Tinubu ta tsara domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya ya kammala
- Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC ya sanar da cewa shirin ya kunshi karfafa sojoji da jami’an tsaro na ‘yan sanda
- APC ta ce Sojojin Najeriya sun kashe sama da ’yan ta’adda da ’yan bindiga 15,000 a shekaru uku kuma za a kara daukar wasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Bola Ahmed Tinubu, ya amince da daukar karin sojoji 28,000 da kuma jami’an ’yan sanda har 50,000 domin a karfafa tsaron kasa.
Shugaban Najeriya ya yi na’am da wannan ne da nufin dakile matsalar rashin tsaro a sassan Najeriya da aka dade ana wayyo Allah.

Source: Getty Images
APC ta kawo sabon tsari na samar da tsaro
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa jiya a cewar jaridar The Cable.
Mai magana da yawun kwamitin, Dele Alake, ya fitar da sanarwa game da hakan a ranar Lahadi.
Matakin na cikin shirin gwamnatin Tinubu na samar da wani sabon tsarin tsaro na shekaru biyar, wanda zai taimaka a yaki da ta’addanci.
Gwamnatin Tarayya na kokarin ganin bayan ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka.
Shirin zai taimaka a inganta ayyukan sojoji, karfafa hukumomin tsaro da kuma tabbatar da samun ingantaccen tsarin tattara bayanan sirri.
A cewar sanarwar, an ji hakan zai taimaka wajen amfani da fasahar zamani a dakile barazanar tsaro.
Nasarorin da sojoji suka samu a shekaru 3
Mista Alake ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata, sojojin kasar sun yi sanadin kashe sama da mayakan Boko Haram da ’yan bindiga 15,000.
Ya kuma yi ikirarin cewa sama da mayakan Boko Haram 130,000 da iyalansu sun mika wuya a karkashin shirin nan na Operation Safe Corridor.
Gwamnati ta samar da shirin ne domin gyara da karbar tubabbun ‘yan ta’adda a cikin al’umma.
Sababbin wuraren horar da sojojin kasa
Ban da sojoji da 28, 000 da za a dauka, The Sun ta ce an samar rundunonin soji guda hudu tare da sake fasalin wasu tsofaffin rundunoni a Najeriya.
An fadada ayyukan sojoji kuma an ba su damar kai dauki cikin gaggawa idan aka samu barazanar tsaro duk a cikin kokarin da gwamnati ta ke yi.
Haka kuma, Tinubu ya amince da kafa sababbin cibiyoyin horas da sojoji guda biyu a Osogbo da ke jihar Osun, da kuma Amasiri-Edda a jihar Ebonyi.
Kowace cibiyar za ta iya horas da sababin sojoji 6,000 a lokaci guda, wanda hakan ke nufin za su iya horas da mutane har 12,000 gaba dayansu.
Sababbin sojoji 28, 000 za a dauka, ana ganin hakan zai inganta tsaro kuma ya rage masu zaman banza.
A bangaren ‘yan sanda kuwa, shugaban na Najeriya ya yarda a samu karin dakaru 50, 000 wanda wannan zai taimaka wajen tsaron cikin gida.

Kara karanta wannan
Gwamna Radda ya yaye jami’an tsaron daji 1008 a Katsina, ya fadi aikin da za su yi
Sababbin alkawuran da Bola Tinubu ya yi
An ji labari APC ta jero alkawuran yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu na ayyukan da za iyi daga 2027 zuwa 2031 idan an zarce a badi.
Jam'iyya mai mulki ta yi alkawarin Inganta wutar lantarki, gina hanyoyi da layukan dogo, bunkasa masana'antu da samar da ayyukan yi a kasa.
Yaki da cin hanci, gyaran harkokin shari'a, karfafa ƙananan hukumomi da inganta ayyukan gwamnati na cikin shirin Renewed Hope Agenda 2.0.
Asali: Legit.ng

