Shugaba Buhari ya cancanci ya zarce a 2019 – Janar Buba Marwa

Shugaba Buhari ya cancanci ya zarce a 2019 – Janar Buba Marwa

Tsohon babban sojan Najeriya, Janar Buba Marwa yayi hira da wata jarida kwanan nan inda ya tabo batutuwa da-dama har yayi kira ga jama’a su sake marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben 2019.

Shugaba Buhari ya cancanci ya zarce a 2019 – Janar Buba Marwa

Janar Buba Marwa yace Buhari zai ci zaben 2019 a Najeriya
Source: Depositphotos

Buba Marwa wanda yayi gwamnan Borno da Legas ya bayyana cewa an samu zaman lafiya kwarai musamman a jihar sa ta Adamawa. A baya Boko Haram ta addabi yankin kafin hawan gwamnatin shugaba Buhari.

Janar Marwa yana ganin cewa shugaba Buhari zai doke kowane ‘dan takara a jihar Adamawa saboda zaman lafiya da aka samu a gwamnatin APC. Marwa yace Buhari zai kuma samu nasara jihohin Arewacin kasar nan.

KU KARANTA: Jama’a ba za su yi nadamar zaben APC ba – Buhari yayi alkawari

Tsohon Jakadan na Najeriya zuwa kasar Afrika ta kudu ya kuma bayyana cewa a tarihin siyasa a kasar nan, babu wanda ya taba samun irin farin jinin Buhari. Marwa yace a 2019, Buhari zai samu kuri’u har a Kudancin Najeriya.

Babban sojan kasar wanda yanzu yayi ritaya yake cewa idan har Buhari ya zarce a kan mulki, za a cigaba da ganin shugabanci na gari tare da hangen nesa da kuma kishin kasa. Yace Buhari mutum ne mai kima a idon Duniya.

Dazu kun ji cewa wani tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja, kuma babban jigo a jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa yana daf da tserewa daga PDP ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel