Sakamakon canji: Aisha Buhari ta karrama mawaka da jaruman Kannywood a fadar shugaban kasa
Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta shirya wani gagarumin taron liyafa a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, inda ta karrama mawaka da jaruman fina finan Kannywood saboda gudunmuwar da suke baiwa gwamnatin Buhari.
Legit.com ta ruwaito an shirya taron ne da hadin kan kungiyar mawakan Arewacin Najeriya domin su bayyana ma Duniya goyon bayansu ga shugaban kasa Buhari a kokarinsa na zarcewa a madafan iko, da kuma canjin daya kawo a kasa.
KU KARANTA: Yadda binciken Sojoji ya kaisu ga bankado inda aka boye gawar janar Alkali
A yayin wannan taro, mawaka da dama sun gabatar da wakoki daban daban na goyon baya ga shugaba Buhari da gwamnatinsa, tare da yaba ma irin aikace aikacen da yake yi ma talakan kasa.
Daga cikin mawakan da suka yi wasa a yayin taron akwai Adam Zango, Alan Waka, Fati Shu’uma, Ado Gwanja, Abubakar Sani, Fati Nijar, Makaho, Jamila Nagudu, da kuma fitaccen mawakin siyasan nan Dauda Kahutu Rarara.
Da take jawabi, babbar hadimar uwargidar shugaban kasa, Hajo Sani, ta bayyana godiyar gwamnatin Buhari ga mawakan da jaruman Kannywood bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatin da kuma rawar da suke takawa wajen yada manufofinta ta hanyar wake wake.
Haka zalika ta jinjina musu saboda cigaba da suke kawowa tare da habbaka masana’antar nishadi ta Najeriya, inda suke goga kafada da kafada da takwarorinsu na kudancin Najeriya.
“Ina jinjina muku wajen kokarin da kuke yin a wayar da kawunan al’umma akan muhimmancin zaman lafiya, da bukatar samar da ingantaccen mulki, haka zalika mun yaba da kokarinku na yayata ayyukan da shugaba Buhari yayi a cikin shekaru uku.” Inji ta.
Shima Adam Zango ya bayyana cewa duk da gudunmuwar da gwamnatin baya ta baiwa Kannywood, amma gwamnatin Buhari itace kan gaba wajen nuna kulawa da masana’antar gaba daya, daga karshe ya baiwa Buhari tabbacin goton bayansu a gareshi a 2019.
Mai gayya mai aiki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron, amma bai dade ba, dayake ba da shi aka fara ba, kuma ya tafi kafin a tashi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng