Aisha Buhari ta karrama wata budurwa da ta nuna kyakyawan hali a wajen aikinta

Aisha Buhari ta karrama wata budurwa da ta nuna kyakyawan hali a wajen aikinta

- Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Buhari ta karrama wata mai shara a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja

- Ma'aikaciyar, Miss ta tsinci jaka makare da dalolin kasashen waje da kudin najeriya cikin ban daki amma ta mikawa hukuma

- Aisha Buhari ta shawarci yan Najeriya suyi koyi da irin wannan kyakyawan halin da matashiyar ta nuna

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta gabatar da kyautar karramawa ga wata ma'aikaciyar Lakewood Development Company, Mary Ishaya da ke aikin shara a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja sakamakon mayar da wani jakan kudi da ta tsinta a ban daki.

A wajen kwarya-kwaryar liyafar da Mrs Buhari da shirya a fadar Aso Villa domin karrama Miss Ishaya, tayi kira ga 'yan Najeriya suyi koyi da irin kyawawan halayen ma'aikaciyar da gaskiya da rikon amana.

Aisha Buhari ta karrama wata ma'aikaciyar filin jirgin sama da ta tsinci kudi kuma ta mayar

Aisha Buhari ta karrama wata ma'aikaciyar filin jirgin sama da ta tsinci kudi kuma ta mayar
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Yadda wasu gwamnonin APC 6 suka shirya makarkashiyar da yasa DSS ta kama Oshiomhole

Idan ba'a manta ba, Kamfanin Dillanci Labarai (NAN) ya ruwaito cewar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN) ta wallafa a shafinta na Twitter @FAAN_Official a ranar 11 ga watan Satumban 2018 cewe, "Muna alfahari da Miss Mary Ishaya da ke aiki da Lakewood Company, wadda aka bawa kwangilar tsaftace filin tashin jiragen sama na Abuja.

"Ta tsinci wadandan abubuwan cikin ban daki: Dallar Amurka 2,000, Dallar Canada 140, kwandaloli 21, N21,850, fasfon fita kasashen waje 2, katin ATM 4, Katin shiga bus 4 a cikin jakka.

"Mai jakar, ma'aikacin Nigerian Deposit Insurance Corporation (NDIC), Imade Uhunwagho tuni ya karbe kayayakinsa."

NAN ta ruwaito kuma cewa kamfanin da yiwa Miss Ishaya karin girma daga mai wanke bayi zuwa mai kula da masu aiki wato Supervisor.

Miss Ishaya ta mika godiyarta ga uwargidan shugban kasan inda ta bayyana cewar karramawar zai sanya ta kara bayar da himma wajen aikinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel