‘Yan wasan Najeriya sun fadawa Aisha Buhari za su goyawa tazarcen Buhari baya

‘Yan wasan Najeriya sun fadawa Aisha Buhari za su goyawa tazarcen Buhari baya

- Wasu fitattun Taurari a Najeriya sun fito sun marawa yakin neman zaben Buhari baya

- Daga cikin wadanda ke goyon bayan tazarcen Buhari akwai tsofaffin 'Yan Super Eagles

- Akwai manyan Mawaka kuma irin su Korede Bello, Jide Kosoko, Iyanya da kuma Silva

‘Yan wasan Najeriya sun fadawa Aisha Buhari za su goyawa tazarcen Buhari baya
Mawaka sun fadawa Aisha Buhari su na tare da Mai gidan ta a 2019.
Asali: Depositphotos

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu karin goyon baya na tazarcen da ya ke nema a zaben 2019 daga wasu manyan Taurari da ake ji da su a cikin Najeriya. Fitattun Taurarin sun yi masa mubaya’a ne ta hannun Mai dakin sa.

A jiya Laraba ne wasu manyan Makada da Mawakan Najeriya su ka karbi lambar yabo daga hannun Uwargidar Shugaban kasa watau Hajiya Aisha Buhari. An yi wannan taro ne na musamman a babban Birnin Tarayya Abuja.

KU KARANTA: Ministan Buhari yayi wa wani Dattijon Arewa kaca-kaca

Manyan Taurarin sun karbi lambar yabo ne daga Kungiyar BSO mai goyon bayan Shugaban kasa Buhari a dalilin kokarin da su ke yi a fannin su na nishadantarwa da wasanni. An kuma shirya taron ne domin yakin neman zaben Buhari.

Tsofaffin ‘Yan kwallon kafa irin su Daniel Amokachi, Peter Rufai, da Garba Lawal su na cikin wadanda aka ba kyautar. Haka kuma Aisha Buhari ta karrama mawaka irin su Korede Bello, Jide Kosoko, Iyanya, Joke Silva da DJ Jimi Jatt.

Daniel Amokachi wanda ya takawa 'Yan Super Eagles leda a shekarun baya ya yabawa kokarin Gwamnatin Buhari na yakar Barayi. Haka kuma Jide Kosoko yace Gwamnatin Buhari ta kawo tsare-tsaren da su ka taba rayuwar jama’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel