Cacar bakin da ake yi tsakanin Aisha Buhari da Shugaban kasa ya sabawa musulunci - Inji Balarabe Musa

Cacar bakin da ake yi tsakanin Aisha Buhari da Shugaban kasa ya sabawa musulunci - Inji Balarabe Musa

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa ya sa baki game da ce-ce-ku-cem da ake ta yi a game da gwamnatin Buhari, inda ake zargin cewa wasu tsirarrun mutane sun katange shugaban kasar.

Cacar bakin da ake yi tsakanin Aisha Buhari da Shugaban kasa ya sabawa musulunci - Balarabe Musa

Bai dace da shari’a Buhari ya rika caca da Matar sa ba - Balarabe Musa
Source: Depositphotos

Hajiya Aisha Muhammadu Buhari tana daga cikin masu ra’ayin cewa akwai mutane 2 ko 3 da su ke juyawa al’amura a Najeriya a bakacin Mai gidan ta, shugaban kasa Buhari. Tuni dai shugaban kasar yayi watsi da wannan zargi.

Balarabe Musa ya bayyana cewa sa-in-sar da ake yi tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mai dakin sa, Aisha Buhari bai dace ba. Tsohon gwamnan kasae yace hasali ma hakan ya sabawa koyarwar addinin musulunci.

KU KARANTA: Yadda aka sa Buhari cikin mari bayan yi masa juyin mulki a 1985

Musa, wanda ya taba yin gwamna a Jihar Kaduna a lokacin mulkin Shehu Shagari yace a shari’ar musulunci, bai sam dace Shugaba Buhari ya rika fitowa a bainar Duniya yana maidawa Mai dakin sa watau Aisha Buhari martani ba.

Tsohon gwamnan yace daga shugaban kasar har mai dakin ta sa, Aisha Buhari, ba su kyauta ba. Musa yace a addinin musulunci, ba a san ma’aurata da kwarewa kan su baya a waje ba, inda yace bai kamata wasu abubuwan su bar gida ba.

Tsohon shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Balarabe Musa ya na mai Allah-wadai da wannan abu da yake faruwa tsakanin shugaban kasar da kuma iyalin sa, inda yace ko a cikin Abokai bai kamata a rika samun irin wannan tonan silili ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel